Gwamnatin Oyo ta rusa gidan da aka ajiye ‘yar uwar Adelabu da ‘yan biyunta da aka sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Oyo ta rusa wani gida mai ɗakin kwana uku da aka yi zargin da shi aka yi amfani wajen ɓoye ƙanwar tsohon Ministan Lantarki, Bayo Adelabu da ‘yan biyunta maza a yankin Lakoun da ke kan hanyar Aiyegun-Olojuoro a Ibadan.

Gidan shi ne wurin da aka tsare Misis Olaide Adegoke John-Paul da an biyun nata ‘yan shekara 12 kafin a kuɓutar da su a ƙarshen mako.

An gudanar da rushe gidan ne bayan wani babban bincike na tsaro da Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Oluwagbemiga Abimbola, ya jagoranta a ranar Lahadi.

A yayin aikin ceto su a ranar Asabar, an harbe ‘yan bindiga guda biyu, yayin da aka kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a lamarin, waɗanda tuni aka gurfanar da su a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Eleyele a Ibadan.

Hukumomi sun cigaba da kira ga mazauna yankin da su kasance masu sanya ido tare da bayar da rahoton duk wani ɓangaren ‘yan bindigar da suka tsere ko wani abin zargi da suka gani a yankunansu.

Hukumomi sun ce matakin ya nuna aike saƙo ga gidajen da aka amfani da su wajen aikata manyan laifuka, lamarin da gwamnati ba za ta lamunta ba.

By Babaji

Leave a Reply