
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin dattawa guda 50 mazauna ƙauyen Magamin Diddi na yankin Magami/Faru da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ne aka yi garkuwa da su yayin zaman sulhu da jagoran ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa Jammo, wanda shi ne jagoran ‘yan bindiga da ke yankin dajin Muntsira a Maradun ne ya yi garkuwa da su.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Bello Dosara, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce tawagar dattawan sun je zaman ne ba tare da sahalewar hukumomin gwamnati ba.
A cewarsa, ‘yan ƙauyen sun yi gaban kansu ne wajen shirya zama da jagoran ‘yan bindiga duk da cewa sun san matsayar gwamnatin jihar game da hakan.
Ya ƙarada cewa, a baya jagoran ‘yan bindigar ya tare hanyar da ke bi a shiga kasuwar ƙauyen, amma ƙaramar hukumar ta riƙa tura jami’an tsaro suna yi wa jama’a rakiya domin shiga da fita kasuwar cikin salama.
Haka kuma, Hon. Dosara ya tabbatar da cewa 11 daga cikin waɗanda aka sacen sun shaƙi iskar ‘yanci, yayin da 39 suke cigaba da zama a komar ‘yan bindigar.
