‘Yan bindiga sun sace dattawa 50 da suka je tattaunawar sulhu a Zamfara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Aƙalla dattawa 50 daga ƙauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun faɗa hannun ‘yan bindiga yayin da suka je wata tattaunawar sulhu da shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Jammo.

Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Bello Dosara, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mutanen sun je ganawa da shugaban ‘yan bindigar ba tare da amincewar gwamnati ba. Ya ce gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ba ta goyon bayan yin sulhu da ‘yan bindiga, amma al’ummar yankin sun yanke shawarar yin hakan da kansu.

A cewar jami’an yankin, Jammo ya amince da tattaunawar ne bayan rikice-rikicen da suka faru tsakaninsa da jami’an tsaron askarawa, inda ɓangarorin biyu suka yi asarar mutane da makamai. Sai dai bayan isar dattawan 50 zuwa sansaninsa, ya ci amanarsu tare da tsare su a matsayin garkuwa. Daga bisani ya saki mutum 11 domin su kai saƙo ga al’umma, yayin da sauran mutum 39 ke ci gaba da zama a hannunsa.

Ɗan majalisar yankin Magami/Faru, Bello Husseini, ya ce shugaban ‘yan bindigar na neman a biya masa naira miliyan 24 domin fansar bindigogi uku da aka ƙwace daga hannun mutanensa a baya. Ya jaddada cewa al’ummar yankin da shugabanninsu ba su amince da sulhu da ‘yan bindiga ba, domin sun tabbatar ba za a iya yarda da su ba. Ya kuma yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ƙaddamar da gagarumin farmaki a dajin Natsira domin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply