Fusatattun matasa sun kori sojojin da aka tura Zurmi a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

A cigaba da samun hare-haren ‘yan ta’adda a wasu yankuna a Jihar Zamfara, wasu fusatattun matasa sun kori jami’an tsaron da aka tura masu a garin Zurmi da ke Jihar Zamfara.

Matasan sun tare hanyar shigowa garin ne suna masu nuna alhinin yadda matsalar tsaro ke ƙara ƙaruwa a yankin.

Sunyi ta jifar sojojin yayin da lamarin ya sanya sojojin suka tsere nan take .

“Matasan sun yi ta cewar bama so, bama yi, azzalumai ne, a cikin kalaman su.

Lamarin ya jefa yankin a cikin damuwa yayin da a halin yanzu babu wani jami’in soja da ke garin.

Lamarin ya biyo bayan harin da ‘yan bindigar suka kai garin na Zurmi da Moriki da wasu sassan ƙaramar hukumar inda aka yi asarar ruyuka da dukiyoyi jiya Lahadi.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin shugaba ƙaramar hukumar daga wakilin mu bai samu ba a yayin haɗa wannan rahoton.

By ukarofi

Leave a Reply