Saudiyya ta jinkirta dawowar alhazan Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

An samu sauyi a jadawalin jigilar dawowar alhazan Jihar Katsina daga ƙasar Saudiyya bayan da hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Saudiyya suka yi gyara a tsarin rabon lokutan tashi da saukar jirage.

Sauyin ya haifar da jinkirin fara jigilar alhazan jihar zuwa Nijeriya, lamarin da ya jawo damuwa a tsakanin wasu daga cikin mahajjatan da ke ci gaba da zaman su a birnin Makkah.

Sakamakon haka, Amirul Hajj na Jihar Katsina a aikin hajjin shekarar 2026, Barista Ahmad Usman El-Marzuq, ya tabbatar wa alhazan jihar cewa an tanadi duk wasu muhimman tsare-tsare na jin daɗinsu, tare da ci gaba da ƙoƙarin ganin an magance matsalar cikin gaggawa.

Barista El-Marzuq ya bayyana hakan ne a wani taron haɗin gwiwa da ya haɗa wakilan tawagar hajjin Jihar Katsina, hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Katsina da ma’aikatan hukumar a birnin Makkah.

Ya ce an tsara fara jigilar dawowar alhazan jihar ne daga ranar 11 ga watan Yuni, sai dai sauye-sauyen da hukumomin Saudiyya suka yi wajen rabon lokutan jirage ya kawo tsaiko ga jadawalin da aka tsara.

Amirul Hajj ya ce an sanar da gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, halin da ake ciki, tare da ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin samun mafita cikin gaggawa.

Ya kuma ce tattaunawar da aka yi da jami’an kamfanin Max Air ta nuna cewa jinkirin ba laifin kamfanin ba ne, illa sakamakon sabon tsarin rabon lokutan jirage da hukumomin Saudiyya suka aiwatar.

Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai daidaita nan ba da jimawa ba, yana mai cewa akwai yiwuwar a bai wa Jihar Katsina ƙarin damar jirgi wanda zai taimaka wajen rage tsawon lokacin jinkirin.

Taron ya kuma tattauna kan rahotannin da ke nuna cewa wasu alhazai sun fara nuna damuwa kan yiwuwar katse musu abinci da masauki sakamakon tsawaita zamansu a ƙasa mai tsarki.

Da yake magana a taron, shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Kabir Bature, ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da samar da abinci da masauki ga alhazan jihar ba tare da wata matsala ba.

Ya ce an riga an sanar da alhazan tun kafin tafiyarsu cewa tsawon zamansu a Saudiyya na iya kaiwa tsakanin kwanaki 35 zuwa 40 gwargwadon yanayin gudanar da aikin hajji.

Bayan taron, tawagar hajjin jihar sun ziyarci manyan otal-otal da ke ɗauke da alhazan Katsina a Makkah, ciki har da na mata, inda suka yi musu bayani kan halin da ake ciki tare da ƙarfafa musu gwiwa da su kwantar da hankalinsu.

Barista El-Marzuq ya tabbatar wa alhazan cewa babu wanda za a hana abinci ko kuma a tilasta masa barin masaukinsa idan zamansu ya wuce ranar da aka fara tsara musu dawowa.

Ya ce tawagar hajjin jihar na ci gaba da tuntuɓar hukumar alhazai ta ƙasa da kamfanonin jiragen sama da hukumomin Saudiyya domin tabbatar da dawo da alhazan cikin mafi ƙanƙanin lokaci.

Amirul hajjin ya kuma yi kira ga alhazan da su ci gaba da nuna haƙuri tare da yi wa Allah addu’ar samun nasarar kammala jigilar dawowarsu cikin sauƙi da nasara.

By ukarofi

Leave a Reply