Kwastom a Apapa ta karɓi harajin tiriliyan N1.8 cikin wata 10

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya reshen tashar ruwa ta Apapa a Legas ta ce ta tara Naira Tiriliyan 1.8 a matsayin kuɗaɗen shiga tsakanin Janairu zuwa Oktoba 2024.

Shugaban Hukumar Kwastom mai kula da yankin Apapa, Babatunde Olomu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin.

Olomu ya ce tara kuɗaɗen shiga na zuwa ne duk da gagarumin koma baya da aka samu a kasuwar.

Ya ƙara da cewa, adadin ya nuna ƙaruwar kashi 101 cikin 100 idan aka kwatanta da biliyan N931 da aka tara a daidai wannan lokacin a shekarar 2023.

“Daga watan Janairu zuwa Oktoba 2024, mun samar da jimillar tiriliyan N1.87 a matsayin kuɗaɗen shiga. Adadin ya haura kashi 101 idan aka kwatanta da biliyan N932bn da aka samu a daidai wannan lokacin a shekarar 2023,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, a watan Oktoba kaɗai, rundunar ta tara biliyan N264, inda ya jaddada cewa adadin shi ne mafi yawan da aka taɓa tarawa a tarihin rundunar.

Hukumar ta bayyana kwarin gwiwar cewa za ta cika kuma ta zarce tiriliyan N2.2 da ta ke nema a shekarar 2024.

By ukarofi