Shugaba Tinubu na iya ƙoƙarinsa wajen yaye wa ‘yan Nijeriya damuwarsu – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan sadarwa da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen wahalar da ‘yan Nijeriya ke fama da shi.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Kaduna a yayin wani shiri na gidan rediyon tarayya na (FRCN) mai suna ‘Hannu Da Yawa’ da ake yi cikin harshen Hausa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN, ya rawaito ministan na cewa cire tallafin man fetur abu ne da ya zama wajibi saboda wasu ‘yan ƙalilan ne ke cin moriyarsa.

Ya ba da tabbacin cewa tattalin arziƙin Nijeriya zai farfaɗo domin babu wata gwamantin da za ta so samun koma-baya a harkokinta.

Ya ce gwamnatin na kowa da kowa ne ba kawai na majalisun ƙasar nan ba, abu ne da ya shafi ɓangaren zartarwa da dukkan ‘yan Nijeriya.

Ya ce a kwanakin baya nan shugaba Tinubu ya ba wa ministoci umarnin rage yawan motocin da suke amfani da su a yayin gudanar da ayyukansu da kuma yawan tafiye-tafiyensu.

“Burin shugaba Tinubu shi ne a barin tsarin da da ake amfani da shi, domin a duk san da muka zauna zaman majalisar zartarwa, shugaba Tinubu na yawan nuna cewa yana so a rage yawan kuɗin da ake kashewa wajen gudanarwa,” in ji ministan.

Sannan ministan ya ce, a ɓangaren noma, Tinubu ya sauya sunan ma’aikatar noma daga ma’aikatar noma da bunƙasa karkara zuwa ma’aikatar noma da wadata ƙasa da abinci domin magance matsalar abinci da ake samu.

Sannan ya ce shugaba Tinubu na ƙoƙarin ganin an magance matsalar tsaro da ake fama da su.

Haka ma batun samar da walwalar jami’an tsaro, ya ce gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin sosai wajen inganta tsarin tsaro a ƙasar nan.

Sannan ya ce shugaban ƙasa na cigaba da nazari kan batun samar da ‘yan sandan jihohi.

A yayin da yake magana kan rashin wutar lantarkin Arewa, Idris ya musanta zargin da al’umma ke cewa an tsara hakan ne domin mai da Arewa baya.

Ya ce babu shugaban da yake da burin ganin al’ummarsa na cikin mawuyaci hali kamar na rashin wutar lantarki kuma shugaban ƙasa na ƙoƙarin samar da hanya mai ɗorewa ta magance matsalar.

“An kusa kammala aikin bututun gas ɗin AKK wanda zai inganta harkokin a Arewa.

Daga nan ya yi kira ga al’umma da su rika faɗar alheri kan Nijeriya dandalin sada zumunta musamman a wannan lokaci da ake yaɗa labaran ƙarya.

By ukarofi