Kyautar da ƙasar Sin ta bai wa duniya ba ƙwayar maganin Artemisinin ba ne kawai

Daga CMG HAUSA

Shekarar 2022 shekara ce ta cika shekaru 50 da gano kwayar maganin artemisinin. Shekaru 50 da suka wuce, masana kimiyya na ƙasar Sin da Tu Youyou ta wakilta, sun gano tare da samun nasarar hako sinadarin artemisinin, wanda ya taimaka wa ƙasar Sin wajen kawar da malariya baki ɗaya.

Ƙasar Sin ta kuma yada wannan magani mai kyau zuwa duniya baki ɗaya. Kimanin mutane miliyan 240 ne a yankin kudu da hamadar Sahara suka amfana da maganin artemisinin, wanda ‘yan Afirka ke kira da “Sihirin magani daga gabas mai nisa”.

Ban da artemisinin, al’ummar Afirka da dama na tunawa da cewa, a lokacin da nahiyar Afirka ta yi fama da annobar Ebola, wasu ƙasashe da yawa sun janye daga yankin da annobar cutar ta ɓulla, amma a nata ɓangaren nan da nan ƙasar Sin ta aike da tawagar likitoci don taimaka wa Afirka, ta kuma aike da muhimman kayayyakin da ake buƙata ga nahiyar, kana sun hada kai kafaɗa da kafaɗa tare da ƙasashen Afirka don yaƙi da cutar har ƙarshe.

A yanzu haka, bil’adama na fuskantar annoba mafi muni da ba a taɓa gani ba shekaru ɗari da suka wuce. Kamar yadda ta ba da gudummawar artemisinin ga duniya, Sin ta ƙara taimakawa duniya tare da ƙaddamar da aikin jin kai na gaggawa mafi girma.

Mataimakin ministan kiwon lafiya na ƙasar Masar Muhammad Hassan ya bayyana cewa, “Ƙasar Sin tana sa himma wajen ba da taimakon rigakafi ga sauran ƙasashe. Sakamakon haɗin gwiwar likitocin tsakanin ƙasashen biyu, adadin al’ummar da aka yi musu allurar rigakafi a ƙasar Masar ya kai kashi 70 cikin 100.”

Daga artemisinin har zuwa alluran rigakafin COVID-19, dukkansu sun rubuta labari iri ɗaya game da yadda ƙasar Sin da duniya ke haɗin kai don kawar da matsaloli. Ƙasar Sin ta sani sarai cewa, ba wai ƙasashe daban daban suna cikin kananan jiragen ruwa sama da 190 ba ne, a’a suna cikin wani babban jirgin ruwa mai makoma daya. A yayin da ake fuskantar matsalar rashin lafiyar jama’a a duniya, ta hanyar gina al’ummar lafiyar bil’adama ta bai daya ne kawai za mu iya shawo kan cutar.

Mai fassara: Bilkisu Xin