2023: Zai zama babban rashin adalci idan ban tsaya takara ba – Osinbajo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin da ta gabata, ya bayyana cewa, rashin adalci ne idan bai tsaya takara a zaven 2023 ba tare da ɗimbin gogewar da ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata yana mulki.

Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo a ofishinsa da ke Akure.

Mataimakin shugaban ƙasan ya yaba da yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa na ɗora masa manyan ayyuka da suka taimaka masa wajen gogewa.

Ya ce, Allah ne ke ɗora mutane kan karagar mulki, amma ya zai zama kamar cin amana ga ƙasarsa idan ya yi ritaya da dak gogewar da ya ke da ita a gwamnati.

Ya yaba wa Akeredolu bisa gagarumin nasarorin da aka samu a jihar.

“Wannan gata ce ta musamman a kira a yi hidima, gata ce ta musamman don yin aiki ko dai a matsayin zartarwa, majalisar dokoki, har ma a matsayin mamba na NWC.

“Na tabbata kowa ya san cewa a hukumance na bayyana aniyata ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a Tarayyar Nijeriya.

“Na yi haka ne a ranar Litinin 11 ga Afrilu, 2022, kuma na yi haka ne, domin da farko babu wanda zai iya jure wa wani abu da Allah bai yanke ba, Allah ne kazai zai iya sa mutum ya zama shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, Gwamna da ma komai a duniya.

“Don haka, na yi imani cewa sai Allah ya yarda za mu komai da mu ke yi, amma na bayyana niyyata a kan farko, kasancewar na yi hidima, kuma cikin yardar Allah na yi hidima na tsawon shekaru bakwai da wasu watanni.

“Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, saboda yadda ya nuna gaskiya da karamcinsa ya tabbatar da cewa an ba ni manyan muƙamai a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, ni ma na yi kamar shugaban ƙasa.

“A wannan matsayi, na san abubuwa da yawa da mafi yawan mutane ba za su tava haɗuwa da su ba, hatta mutanen da ke cikin gwamnati ba za su tava haɗuwa da su ba kuma na samu awarewa sosai a kan hakan.

“Sau da yawa shugaban ƙasa idan ba ya nan, ya kan ce min, ba na so in yi maka katsalandan ta kowace hanya, a matsayinka na muƙaddashin shugaban ƙasa, kai ne shugaban ƙasa, ka tabbata kana ka yi adalci, kar ka koma zuwa gareni wani abu, kar ka yi min tambayoyi, kawai ka yi duk abin da ka ke buƙatar yi.

“Zai zama babban rashin adalci ga ƙasarmu, shi ya sa na jefa hulata cikin zobe tare da tabbatar da cewa na gabatar da mafi kyawu a kan muƙamin Shugaban Tarayyar Nijeriya,” inji shi.

Tun da farko, Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya yaba wa mataimakin shugaban ƙasar bisa ziyarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *