‘Allah ya ba mu shugabanni adalai’, addu’ar Ali Nuhu ga Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, ya yi addu’ar samun shugabanni adalai kuma masu jin ƙai ga Nijeriya.

Jarumin ya yi wa ƙasarsa waɗannan addu’o’i ne yayin hajjin Umarah da ya tafi kamar yadda saƙon da ya wallafa a shafinsa na facebook ya nuna.

An ga Ali Nuhu tare da ɗansa Ahmad cikin harami a wasu hotuna da ya wallafa a shafin nasa na Facebook.

Ali Nuhu ya yi addu’a da cewa, “Allah Ya karɓi ibadunmu, ya inganta rayuwarmu, ya sanya wa kasuwancinmu albarka, ya raya zuri’armu bisa tafarki madaidaici.

Ali Nuhu tare da ɗansa Aahmad

“Ya kawo mana ƙarshen tashin hankalin da ƙasarmu ke fuskanta, Ya ba mu shugabanni adalai kuma masu jin ƙai, Ya yafe mana zunubanmu.

“Ya ba mu ikon taimakon mabuƙata, Ya ɗaukaka addininmu, Ya kuma sa Aljanna ce makomarmu.”