Wajibi ne Afirka ta yi shirin tunkarar yunwar da za ta kunno kai – Adesina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka (ADB), Akinwumi Adesina ya gargaɗi ƙasashen Afirka cewa su gaggauta bazama wajen bunƙasa noma, domin su samu abincin da za su tunkari yunwar da za ta buwayi duniya, nan ba da daɗewa ba.

Adesina ya ce, “tilas Afirka ta yi shirin tunkarar gagarimar yunwar da babu makawa sai ta darkako duniya.”

Da ya ke amsa tambayoyin wasu fitattun manema labarai a Babban Taron Cibiyar Afirka ta Atlantic Council, ya ce ƙasashen Afirka da za su fi jin jiki su ne waɗanda rikice-rikice da tashe-tashen hankula suka fi yi wa katutu, waɗanda canjin yanayi ya gigita da waɗanda suka samu gurguntakar tattalin arziki sanadiyyar ɓullar cutar Korona.

Ya ce aƙalla Korona ta yi sanadiyyar mutum miliyan 30 sun rasa aikin su a Afirka.

Adesina ya ce yaƙin Rasha da Ukraniya ya haifar da bala’in ƙunci a Ukraniya, sannan kuma ya na haifar da raɗaɗin tsadar rayuwa a sauran sassan duniya, ciki har da Afirka.

Ya ce Rasha da Ukraniya ke samar da kashi 30 bisa 10 na alkamar da ake sarrafawa ana yin kayan abinci a duniya.

“To yanzu farashin alkama a duniya ya tashi da qarin kashi 50 bisa 100.

“Wannan tsadar kuwa rabon da duniya ta fuskanci irin wannan tsadar kuwa, tun cikin 2008.

“Nan da watanni kaɗan farashin takin zamani, wutar lantarki da kayan abinci zai ƙara munana a Afrika.

“Kashi 90 bisa 100 na kayan da Rasha ta sayar Afirka cikin 2020, duk alkama ce, har ta dala biliyan 4. Ukraniya kuwa ta sayar wa Afirka alkama ta dala biliyan 3 da kuma masara.

“Don haka tunda yanzu yaƙi ya hana wannan cinikin, tilas ƙasashen Afirka su bazama wajen noma kayan abincin da zai hana guguwar yunwa domin tunkarar ƙarancin abinci ya darkako duniya gadan-gadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *