Rashin haihuwa: Laifi matar ne! (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

To ko laifi ta ne, ko ba laifi ta ba ne, a ƙasar Hausa da wasu wurare a Afirka sun ce laifin matar ne rashin haihuwa. To maimakon a dinga nuna yatsa ga wani a ce laifinsa ne matsalar haihuwa, me zai hana a  yi ninƙaya a kogin bincike a samo mafita? Don muna ganin abubuwa da dama a rayuwar zahiri. Inda za ka ga mace tana zaune shekara da shekaru da namiji ba haihuwa, amma tana fita daga gidansa, ta yi wani auren, sai ka ga ta samu haihuwar. Idan mai rabon tagwaye ce ma har da tagwayen za ka ga ta samu. Don haka, ga wasu hanyoyi da za a magance matsalar rashin haihuwa a gidan aure maimakon a nuna wa juna yatsa.

Babbar mafita ta farko ita ce, a fara bin hanyoyin maganta matsalar rashin haihuwar. A je asibiti ko wajen masana a gano ma menene ainihi abinda ya hana samun haihuwar, kuma a magance shi a likitance ko a gargajiyance. Sannan a dinga haɗawa da addu’a sosai don samun mafita. In dai ba ƙaddararku ce Allah ya rubuto muku rashin haihuwa a rayuwarku ba.

Abu na biyu, a kwantar da hankali a yarda da ƙaddara. An san rashin haihuwa da ciwo don ciwo. Musamman ma idan kuna kwatanta kanku da wasu da kuke ganin suna samun haihuwar a sauƙaƙe, wasu ma har tsayar da haihuwar suke saboda ta yi musu yawa. To ke ƙaddararku ce a haka, ki yi imani da ita. Duk da dai za ki nemi sauƙi kamar kowacce cuta, amma kar ki san ran dole sai kin samu biyan buqata. Domin rayuwa ɗayan biyu ne. Ko ka samu a nan Duniya ko Lahira. Kuma ki dinga duba sauran ni’imomin da Allah ya yi muku da bai yi wa wasu masu haihuwar ba. 

Na uku, a kawar da damuwa. An san damuwa dole ce ga ma’aurata da suka jima ba su samu rabo ba. Amma a yi ƙoƙarin ɗauke kai daga samuwar kamar a shiga makaranta ko aiki ko sana’a ko ma islamiyya don ɗauke muku kewa ta rashin haihuwa. Yawan damuwar za ta iya jawo muku cututtuka masu alaƙa da rashin kwanciyar hankali da damuwa kamar, hawan jini ko ‘depression’.

Na huɗu, kada ku dinga zargin juna. Ita rashin haihuwa ba laifin kowa ba ne daga cikin ma’aurata sai jarrabawar Ubangiji. Idan aka ɗauki tashin shekaru ba a haihu ba, ma’aurata sukan shiga yanayi na damuwa da  ɓacin rai har ma da nuna wa juna yatsa wanda hakan sam bai dace ba. Musamman tunda ba laifin kowa ba ne a cikinku. Tunda kowannenku shi ma yana cike da damuwar rashin haihuwar. Dangin miji wani lokacin saboda jahilci ko don zuciya sukan tisa matar ɗan uwansu a gaba, su yi ta mata gori da habaice-habaice, har ta ji kamar ta mutu ma ta huta gabaɗaya. Sannan saki ma  ba mafita ba ce. Dom idan an sake ta Allah zai iya hana ka haihuwar ko kuma ya saka mata ta wani ɓangaren da ba ka tava zato ba.

Don haka, nadama kan iya biyo baya. Haka wani lokacin akan yi wa mace kishiya saboda rashin haihuwa. Idan an samu biyan buƙata kuma sai a wulakanta mara haihuwar. Alhali ita ma ba laifi ta ba ne. Wataƙila ta fi kowa ma jin zafin rashin haihuwar.

Takan shiga damuwa har ma ta faɗa cikin savon Ubangiji idan ba mai ƙarfin imani ba ce. Don haka, kamata ya yi namiji ya tsaya wa matarsa a yayin da danginsa ko kishiyoyinta suke tsangwamar ta a kan rashin haihuwa.

Na biyar, matar da ba ta haihuwa tana buƙatar jin sauraren wa’azizzika da tarihin magabata don su ƙarfafe ta. Haka yana da kyau dangi da abokan arziki har ma da mijinta su dinga yi mata nasiha da ban baki don hankalinta ya kwanta don rashin haihuwa akwai ciwo ba kaɗan ba. Kuma ko ba komai hadisi ingantaccen ya zo da cewa, ka yi wa mutum magana ta nasiha mai daɗi tana daga sadaka. 

Na biyar, a matsayinka na namiji kada ka yi amfani damarka yadda bai dace ba. An san Allah ya hore maka damar aurar mata fiye da ɗaya har zuwa huɗu. Idan matarka ba ta haihuwa, ka duba girman Allah idan ka yi aure ka samu haihuwa ka yi adalci tsakaninsa da ita da mai haihuwar. Wanda ya ji ƙan wani bai san shi ma inda Allah zai ji ƙansa ba. Watsi da ita zai ƙara mata damuwa a kan damuwarta ta rashin haihuwa. 

Na shida, idan akwai wata ƙungiya ta mata marasa haihuwa ya kamata ki shiga don jin labaran su  da hanyoyin da ba ki sani ba. 

Na bakwai, kada ku guji abokan rayuwarmu saboda rashin haihuwa. Namiji duk da kana da damar yin saki a wannan yanayi ka ji tsoron Allah. Don ba ka sani ba ko matsalar daga kai ne. Kuma kana da ƙanne mata kuma Allah zai iya ba ka yara mata ba za ka so a sako maka su a kan laifin da ba su aikata ba ko wata ƙaddara da Allah ne ya ɗora musu ba. 

Na takwas, kar a sare ko a gaji. Ku fawwala wa Allah komai a sakankance in dai da rabo za a haihu. Domin mai nema yana tare da samu. In da rai, da rabo. A cigaba da neman magani da addu’a har Allah ya sa a dace. Amma ku sani, za kuma a iya ƙin samun biyan buƙata. Shi ma wannan jarabawa ce daga Allah, Shi yake yadda ya so.

Na goma, kada ki damu, ki ɗora wa kanki laifi ki tsangwami kanki saboda rashin haihuwa. Duk wanda ya takura miki, ya gaya miki inda ya sayi nasa ‘ya’yan ke ma ki je ki saya a can. Ki yi sha’aninki haihuwa idan Allah ya so za ki samu. Idan ba ki da rabo, duk ɓacin rai da tashin hankalinki ba za su sa ki samu ba. 

Na goma sha ɗaya, ki kasance mai shagaltuwa da wasu abubuwan, ba wai ki yi ta damuwa da rashin haihuwa ba. Ki shagaltu da sauran abubuwa ki ci mai kyau, ki sha  mai kyau, ki yi kwalliyarki ki fito. Ki yi harkokinki, ki kula da kanki sosai. Rashin haihuwa ba kanki farau ba. Kuma idan kina da rabo za ki samu. 

Na sha biyu kuma, ‘yaruwa ki duba girman Allah ki zama mai tsoron Allah kada son haihuwa ya sa ki kauce hanyoyin Allah. Ki zama mai tsoron Allah ki karvi ƙaddararki. Allah ya san da ke, kuma shi zai yi miki tagomashi ta wani ɓangaren na rayuwar Duniya ko Lahira. 

A nan za mu tsaya, sai wani makon a filinmu na Zamantakewa a jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. Ina godiya da masu kira don fatan alkhairi da shawarwari. Haƙiƙa kuna ƙarfafa ta. Na gode.