Rashin haihuwa: Laifin matar ne!

Daga AMINA YUSUF ALI

Wai da ma laifinta ne? Kamar yadda al’ummomim Duniya suke yin aure saboda wasu dalilai da suke ganin sun yi musu kamar neman ƙarfi, ko saboda soyayya kawai ko arziki da sauransu. Amma a ƙasar Hausa babban maƙasudin yin aure shi ne samun haihuwa. Samun haihuwa na ɗaya daga cikin nasarorin da Malam Bahaushe yakan ƙirga daga cikin nasarorin zaman aure. Da zarar ma’aurata suka yi aure, ba abinda su da ‘yanuwa da abokan arziki da sauran al’umma suke jira irin su ga an samu ƙaruwa, wato haihuwa. Daga zarar shekara guda ta wuce an ji shiru, sai a fara tunanin lafiya? Shekaru biyu zuwa sama kuma, sai a fara zargin akwai matsala. Amma a al’adar ƙasar Hausa har ma a al’adar sauran ƙabilun Nijeriya idan an samu rashin haihuwa, to matsala da laifin matar ne ba mijin ba. Musamman zamanin da ba a san a je asibiti don yin bincike da gano inda matsalar take ba. Akwai dalilai da dama da suke jawo matsalar rashin haihuwa a tsakanin ma’aurata kamar:

*Rashin cikakkiyar lafiyar haihuwa ta ɗaya daga cikin ma’auratan ko dukkansu. Idan an samu wata tawaya ta halitta daga ɓangaren sassan da suke taimakawa wajen haihuwa. Wani lokacin kuma mijin ne ba shi da ƙarfin ƙwayoyin halittar da zai iya samar da ɗa. Wasu daga waɗannan matsaloli kuma da a ce za a je asibiti ko a je wajen masana a duba ma’auratan, za a iya shawo kansu.

  • Ƙaddara: kamar yadda Allah yake rabon arziki da mutuwa haka yake rabon ‘ya’ya ma. Saboda haka, arziki da haihuwa dukka suna hannun Allah. Duk wanda Allah bai nufa zai samu ba, ba zai taɓa samu ba ɗin. Amma kuma ba wai don Allah bai ba su ba yana nufin Allah bai tanadar musu wani babban rabo a ranar gobe ba.

*Lokaci: Akwai waɗanda Allah bai nufe su da haihuwa a farkon ƙuruciyarsu ba sai tukunna idan shekaru sun fara tafiya za a ga Allah yana ta ba su. Su nasu kawai jinkiri ne.

*Cima da yanayin halitta da muhalli: Su ma dukka suna kawo rashin haihuwa ko samunta. Misali wani bincike ya taɓa nuna cewa, matan Yarabawa sun fi kowa haihuwar tagwaye a Nijeriya saboda suna yawan cin doya da rogo.

*Abokin rayuwa: Akwai mutanen da suke da halitta ta musamman da ba da kowacce mace suke iya ƙyanƙyashe ƙwan haihuwa ba sai ƙalilan. Irin haka ne sai a ga mutum matansa uku ko fiye, amma guda ce kaɗai take haifa masa zuriyya. Wasu matan da za su fita su yi wani auren sai a ga sun haihu. Son ba haihuwar ce ba sa yi ba. Wani kuma mijin ne ma ba ya haihuwar gabaɗaya.

*Ciwon sanyi: Ciwon sanyi a mata ko maza yana matuƙar taimakawa wajen daƙile samun ciki. Don haka, ma’aurata musamman mata su dage da maganin ciwon sanyi.

*Yawan ɓari: Yawan ɓari musamman idan ba a yi wa mace wankin ciki idan ta yi, yana hana wani cikin zama tare da lalata shi.

*Gado: Shi ma rashin haihuwa ana gadonsa wajen iyaye. Miji ko mata za su iya gadon rashin haihuwa daga iyaye, kakanninsu ko dangi.

*Rashin aƙidar rayuwa ta gari. Misali kamar rashin samun hutu ko rashin motsa jiki, ko cin abincin da zai iya haifar da ƙiba mai yawa da sauransu.

*Rashin dai-daituwar al’adar mace da ciwon mara da sauransu. Matan da ba sa haihuwa idan aka bincike su za a ga al’adarsu ba ta tafiya bai-ɗaya. Ko kuma suna fama da matsananciyar ciwon mara yayin al’ada.

Waɗannan su ne wasu daga cikin dalilan da kan jawo rashin haihuwa tsakanin ma’aurata. Matan auren da ba su haihu ba a ƙasar Hausa da ma wasu sassa na ƙasar nan suna fuskanta ƙalubale da uƙuba mai yawa. Wasu daga cikin ƙalubalen sun haɗa da:

Na farko akwai zargin rashin samun haihuwar saboda sun riga sun yi yawon bariki kafin su yi aure. Ana zargin ma sun sha zubar da ciki ne shi ya sa yanzu mahaifarsu ta lalace suka kasa ɗaukar ciki. Ko kuma Allah ne ya tashi yi musu hukunci ya hana su haihuwar. Ko kuma a dinga zargin yawan tsarin iyalin ne kafin su yi aure ya jawo musu matsalar.

Abu na biyu kuma, ana zargin wasu matan kawai sun ƙi yarda su haihu a gidan da suke ne. Wato dai suna yin tsarin iyali ko zubar da ciki a voye. Irin wannan zargi ya sha kawo mutuwar aurarraki ko samun tashin hankali a tsakanin ma’aurata. Namiji Bahaushe ya ɗauka in dai mace ta ƙi haihuwa da shi, ba ta sonsa ko kuma tana son fita daga gidansa ta auri wani ne.

Uƙuba ta uku da irin waɗannan mata kan fuskanta shi ne, a ƙaro musu kishiya. Namiji ko ya haƙura da ƙaddarar rashin haihuwar danginsa mata za su yi ta tunzura shi har sai ya ƙaro aure. To ba ma ƙarin ne abin ji ba, rashin adalcin da za ta fuskanta a matsayinta na mace mara haihuwa. Idan ba dace ta yi da miji mai tsananin sonta ba, ko mai ilimin islama mai zurfi ko kuma mai fahimta mara son zuciya ba.

Matsala ta huɗu kuma, macen da ba ta haihuwa namiji zai iya sakin ta duk lokacin da ya yi niyya. Domin da yawa maza suna tsoron sakin mace ne saboda ba su san yadda za su yi da yaran da suka haifa tare da ita ba. Amma ita mace mara yara ta fi sauƙin a sallame ta.

Matsala ta biyar ita ce, idan mace ba ta haihuwa, kuma ko da ta yi zama mai tsaho da namiji, to fa bayan ransa danginsa za su iya ƙwace gadonta su hana. Idan kuma da wata matar ko wasu matan masu ‘ya’ya, ai sai yadda hali ya yi. Ba lallai ne a ba ta gadonta yadda Allah ya tsara ba. Sai dai an samu masu tsoron Allah kawai.

Sannan kuma abu na shida shi ne, mace mara haihuwa tana shan gori kashi-kashi. Wani lokacin a wajen dangin miji, ko kishiyoyi, har ma da al’ummar gari da ba su haɗa komai da su ba. Kowa saboda raini yana ganin zai iya gaya mata maganar da ya yi niyya.

Juna biyu

Sannan uƙuba ta ta bakwai akwai ƙyama musamman daga miji ko danginsa ko al’ummar gari. Mace idan an san ba ta haihuwa, ba kowa zai iya aurenta ba. Ko zuri’arsu ne aka samu wanda ba ya haihuwa sosai, to ta zama abin ƙyama.

Matsala ta gaba kuma ita ce, wata macen rashin haihuwa kan zama mafarin aure-aurenta. Domin za ta yi ta tsalle daga wannan gidan aure zuwa wani ko za ta dace ta samu rabon haihuwa.

Sannan mace mara haihuwa kullum a cikin kaɗaici take da tsarguwa. Ko yaya aka ɗan yi mata wani abu game da yara, sai ranta ya sosu ta dinga ganin saboda ba ta haihu ba ne. Ko da kuwa wanda ya yi matan bai san ya yi ba.

Mace mara haihuwa kan zama koma-baya a gida a wajen miji da kuma sauran mata masu ‘ya’ya. Idan ba namiji mai tsoron Allah ko kishiyoyi masu tsoron Allah ba, to za ta yi ta fuskantar rashin adalci kala-kala.

Haka ita ma matar mara haihuwa idan ba tawakkali gare ta ba, za ta iya kamuwa da cututtuka mugaye da suka shafi damuwa kamar cutar hawan jini ko ta damuwa (depression) da sauransu. Haka idan ba ta kai zuciya nesa ba, za ta iya sanya kanta a halaka don ganin ta samu biyan buƙatar samun haihuwa. Ita ce ‘yan tsibbu da bokaye, duk idanunta sun rufe ba ta ji balle gani.

Amma abin mamakin maza ba su fiye gorin haihuwa ba, mata su ne suka fi yi musamman dangin miji da kishiyoyi. Za mu cigaba a mako mai zuwa. Mu haɗu a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini ta Manhaja Blueprint.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *