Wakilin Sin ya buƙaci a kawo ƙarshen sabon yaƙin cacar baka

Daga CMG HAUSA

Jakadan ƙasar Sin a ƙasar Amurka Qin Gang, ya buƙaci a dauki matakan da za su warware taƙaddamar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka wanda ke neman rikiɗewa zuwa wani sabon yaƙin cacar baka.

Qin ya yi wannan tsokaci ne a yayin gabatar da jawabi a taron dandalin tattaunawa kan ƙasar Sin na kwalejin Harvad na HCCF ta kafar bidiyo.

Ya bayyana cewa, jami’ar Harvard tana da ɗalibai Sinawa sama da 1,000, adadi mafi yawa na ɗalibai ‘yan ƙasashen waje, ya bayyana lamarin a masayin wata alama dake bayyana ruhin alaƙa a tsakanin mutum da mutum tsakanin ƙasashen Sin da Amurka.

Sai dai kuma, Qin ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin ƙasashen biyu tana ƙara fuskantar yanayi mai sarƙaƙiya, da ƙara tabarbarewar dangantaka, da kuma rashin fahimtar juna dake ƙara kamari a tsakanin ƙasashen biyu, wanda ke neman zama tamkar wani sabon yaƙin cacar baka.

Qin ya ce, yana fatan dandalin zai yi amfani da hikimomi, da kuma gabatar da muhimman shawarwari daga ɓangarorin biyu domin tattauna su, tare da lalubo bakin zaren warware saɓani da rashin fahimta dake wanzuwa a tsakanin manyan ƙasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Dandalin tattaunawa kan ƙasar Sin na kwalejin Harvard wanda aka kafa a shekarar 1997, ya kasance dandalin dalibai mafi girma kuma mafi daɗewa dake ba da damar tattaunawa don ƙara wa juna sani game da hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka. Ana gudanar da taron dandalin ne a duk watan Afrilu a jami’ar Harvard.

Fassarawa: Ahmad Fagam