Wang Wenbin: Amurka na ƙara zama ƙasa da ake keta haƙƙin bil Adama a cikinta

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matuƙar damuwa game da yanayin taɓarɓarewar haƙƙin bil adama a Amurka, inda shaidu da dama ke nuna yadda batun nuna wariyar launin fata, da laifuka masu alaƙa da harbin bindiga, da yadda jami’an tsaro ke amfani da ƙarfi fiye da kima ke ƙara ta’azzara.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Litinin din nan, ya ce waɗannan laifuka masu nasaba da keta haƙƙin bil adama sun jima suna gudana, sun kuma ratsa dukkanin sassan ƙasar.

Jami’in ya ce a bana ake cika shekaru 30, tun bayan da ƙasar Sin ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a karon farko. Kuma a yanzu Sin ta zamo ƙasa ta 2, mafi ba da tallafi ga ayyukan na MDD, kana ƙasa ta ɗaya wajen tura dakaru cikin tawagogin MDDr, tsakanin dukkanin ƙasashe mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD.

Daga nan sai Wang ya bayyana aniyar ƙasar Sin, ta ci gaba da aiki tare da dukkanin ƙasashe masu son zaman lafiya, wajen ingiza ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya.

Mai fassarawa: Saminu