Kamfanonin ƙasar Sin da ke Masar sun bai wa mabuƙata gudunmawa a watan Ramadan

Daga CMG HAUSA

Rahotanni daga ƙasar Masar na cewa, sama da kamfanonin ƙasar Sin 30 da ke ƙasar ne, suka yi amfani da damar watan Ramadan, wajen shirya taron jin kai a birnin Alƙahira ranar Asabar ɗin da ta gabata, domin ba da gudummawar Fam miliyan 1 na ƙasar Masar, kwatankwacin dalar Amurka dubu 54,245, don taimakawa iyalai dake wurin waɗanda ke cikin mabuƙata.

A cewar masu shirya taron, bikin na bana shi na takwas, tun bayan da majalisar ‘yan kasuwa ta ƙasar Sin ta ƙaddamar a ƙasar Masar a shekarar 2015. A cikin waɗannan shekaru, gudummawar akwatunan kyaututtuka na Ramadan fiye da 10,000 da majalisar ke bayarwa, sun taimakawa sama da iyalai 40,000 da ke fama da talauci.

A jawabinsa yayin bikin, jakadan ƙasar Sin dake ƙasar Masar Liao Liqiang ya bayyana cewa, al’ummar ƙasar Sin suna martaba dabi’ar gargajiya ta karramawa da mayar da alheri, kana kamfanonin ƙasar Sin, suna koyi da wannan al’ada wajen ba da taimako dake nuna kyakkyawar abota da aminci a tsakanin al’ummomin ƙasashen biyu.

A nata jawabin shugabar ƙungiyar raya haɗin kai ta ƙasar Masar Hanaa Ismail, ta gode wa bangaren ƙasar Sin da shirya wannan biki, tana bayyana cewa, za a raba tallafin ga mabuƙata a kan lokaci.

Fassarawa: Ibrahim Yaya