Ayyukan mazaɓu: Yadda wasu sanatoci suka yi sama-da-faɗi a mazaɓunsu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta yi cikakken bayani kan yadda ake zargin wasu sanatoci guda uku daga jihohin Kebbi, Taraba, da Jigawa da sama-da-faɗi da kuɗaɗe a ofishinsu tare da mayar da kadarorin jama’a zuwa ga amfanin kansu wajen gudanar da wasu ayyukan mazaɓu na miliyoyin naira.

A cewar hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa, ’yan majalisar sun bada kwangilar gudanar da wasu ayyukan mazaɓu da suka gabatar wa gwamnati inda su, danginsu ko abokan hulɗarsu ke da muhimmin kaso kai tsaye ko a kaikaice.

“A wani lamari da ya taso da rikici, an yi zargin cewa ’yan majalisar sun yi amfani da ɗaukar tasiri a kan hukumomin zartarwa don ba da kwangilar ga kamfanonin da ’yan majalisar suka mallaka, iyalansu ko abokan hulɗarsu,” inji ICPC a wani rahoto na binciken ayyukan mazaɓar ta.

“An lura da al’amuran cin amanar ofis da wasu masu tallafawa da jami’an hukumomin zartarwa suka yi a lokuta da dama,” rahoton da ke ɗauke da binciken farko na kashi na biyu na ‘ICPC Constituency and Executive Projects Tracking Initiative’ (CEPTi), a wani ɓangare.

Rahoton ya kuma bayar da misali da yadda aka mayar da ayyukan jama’a zuwa amfanin kansu da motoci da na’urorin ruwa da aka kwato daga harabar ’yan majalisar dattawan ko kuma alaƙarsu.

Rahoton ya ce, an bi diddigin ayyukan samar da ayyukan yi na shiyyar guda 490 (ZIP), wanda aka fi sani da ayyukan mazaɓu, a kashi na biyu na CEPTi, wanda ya bankaɗo wasu laifuka da ake zargin ’yan majalisar tarayya da aikatawa tare da haɗin gwiwar wasu jami’an ma’aikatun da ke aiwatar da aikin a sassan daban-daban na hukumomin gwamnatin tarayya.

Rahoton ya kuma bankaɗo cin amana iri-iri a wasu ayyuka 232 na zartarwa da aka bi diddigin a lokacin kashi na biyu na CEPTi wanda ya fara a watan Yunin 2020, yana daf da matakin farko na atisayen da ya gudana a shekarar 2019.
Kowanne daga cikin ayyukan ZIP 490 da aka bi diddigin, a cewar ICPC, an kashe Naira miliyan 100 zuwa sama da haka.

ICPC ta ce, yayin da aka ware kimanin Naira Tiriliyan 2 ga ZIP tun daga shekarar 2000, ’yan ƙasar na cigaba da kokawa da kammala aikin, rashin kammalawa ko kuma rashin wanzuwar waɗannan ayyuka a yankunansu.

Hukumar ta kuma bayyana yadda wasu ’yan majalisar suka gudanar da ayyukan da suka hana ’yancin jama’a da halascin ayyukan.

Ayyukan da suka haɗa da samar da ababen hawa da kuma ɗaruruwan injinan fanfo har zuwa gine-gine, an yi su ne a yankunan Kebbi ta Tsakiya, Jigawa ta Kudu maso Yamma, da kuma yankin Taraba ta Kudu.

Ba a ambaci sunayen ‘yan majalisar da hukumar ICPC ta ba da tutar ayyukan mazaɓarsu a cikin rahoton ba.

Senator Emmanuel Bwacha, Taraba ta kudu shi ma wani ɗan majalisar tarayya ne mai wakiltar Taraba ta kudu Emmanuel Bwacha ya bada kwangilar gine-gine tare da gyara tubalan ajujuwa a makarantar ma’aikatan jami’ar tarayya da ke Wukari ga kamfaninsa.

A wani labarin kuma, an zargi Sanatan na Taraba da karkatar da kwangilar samar wa ma’aikatu ruwa a mazaɓarsa.

Da ake zargin an mayar da ayyukan jama’a zuwa amfanin kashin kai, binciken ICPC ya nuna cewa Mista Bwacha wanda ya ɗauki nauyin sayen ma’aikatan ruwa a mazavarsa a yankin Sanatan Taraba ta Kudu ya mayar da irin waɗannan kayayyaki zuwa amfanin kansa.

“Kamfanin da ba a tava raba su ba kafin hukumar ta sa baki, an sayo su aka kai su ga mai ɗaukar nauyin (Mr Bwacha), kuma an same su a hannun wanda ya ɗauki nauyin; da aka yi ciniki da kuma biyan kuɗin da aka samu a asusun bankin mai ɗaukar nauyi,” inji rahoton ICPC.

Rahoton ya ƙara da cewa, daga baya jami’an CEPTG sun kwato rijiyoyin ruwa guda biyu tare da kayan tallafi da kuma wata tankar ruwa guda ɗaya wanda mai ɗaukar nauyin ya mayar da shi na ƙashin kans daga hannun Sanata.

An zaɓe shi a ƙarƙashin jam’iyyar PDP don wakiltar mazaɓar Donga/Ussa/Takum na jihar Taraba a majalisar wakilai a 2003. Ya kasa sake tsayawa takara a 2007.

Amma ya sake dawowa a shekarar 2011 ya zama Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu Sanata. An sake zaɓen Bwaha a majalisar dattawa a shekarar 2015, sannan a shekarar 2019.

A matsayin sanata da aka zaɓa a jam’iyyar PDP, Bwacha ya zama mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa a farkon majalisar wakilai ta tara a yanzu amma ya ajiye muƙamin bayan ya koma APC mai rinjaye a watan Fabrairu.

Haka zalika, ICPC ta zargi Sabo Mohammed mai wakiltar Jigawa ta Kudu maso Yamma, da karkatar da kwangilar samar da ma’aikatan ruwa ga mazaɓarsa.