Kano 2023: Zan yi takara ba gudu ba ja da baya – Sheikh Ibrahim Khalil

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban Majalisar Malamai na Kano da Arewacin Nijeriya, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce, babu gudu babu ja da baya kan batun tsaya wa takararsa wajen neman gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin tutar jam’iyyar ADC a zaɓen 2023 mai zuwa.

Sheik Khalil ya bayyana haka ne lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan tunawa da Malam Aminu Kano, wato Gidan Mumbayya, dake Unguwar Gwammaja a ƙaramar Hukumar Dala a Birnin Kano.

Shehin malamin ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowarsa daga taron raba kyaututtuka ga sama da mutane 80 da suka nuna basira wajen iya rubutu a wani shiri da su ke sauraro a gidan rediyon Kano, wanda malamin yake gabatarwa.

Haka zalika, ɗan siyasar kuma malamin addinin Musulunci, ya bayyana cewa wanna gasa ko tambayoyi da aka yi wa masu sauraro a tsawon lokuta da kuma amsa tambayoyin da suka yi, ya nuna cewa kowane mutum zai iya bada tasa gudunmawar in an bashi dama.

A ƙarshe Shugaban Majalisar Malaman na Arewacin Nijeriya ya yaba wa waɗanda suka shiga gasar rubutun da kyakyawar fahimta, inda kuma ya yaba wa ɗaukacin masu sauraron shirin, da kuma waɗanda suka bada gudunmawar kyaututtuka ga marubutan, wanda ya haɗa da kyautar kujerar Makka, ga wanda ya zo na ɗaya da sauran kyaututtuka masu alfarma ga ɗaukacin marubutan na fahimta fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *