Kakakin Majalisar Bauchi ya yi wa APC sakin da babu kome

Daga BASHIR ISAH

Kakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Y. Sulaiman ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyya mai mulki a jihar, PDP.

Da yammacin Asabar da ta gabata Sulaiman ya bayyana ficewar tasa a fadar gwamnatin jihar a lokacin da suke buɗa baki tare da Gwamna Bala Mohammed da wasu ƙusoshin PDP daga yankunan ƙananan hukumomin Ningi, Toro, Warji da kuma Dass a jihar.

Abubakar Sulaiman ya ce ya yanke shawarar komawa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ne saboda kyakkyawar fahimta da kuma jin daɗin aiki tare da Gwamna Bala, kana ya yi alƙawarin ci gaba da yin aiki tare da gwamnan don amfanin jihar.

Da yake jawabi, Kakin ya ce, “Ina mai amfani da wannan dama a yau don in bayyana a hukumance cewa ina tare da mai girma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed a jam’iyyar PDP.

“Ɗaya daga cikin dalilaina na komawa PDP shi ne la’akari da salon mulkin gwamnanmu da kuma jajircewarsa wajen bunƙasa jihar.”

Daga nan, Kakakin ya yaba wa Gwamna Bala bisa kyakkyawar dangantakar aiki tsakaninsa da majalisar dokokin jihar da ya nuna wanda a cewarsa hakan ya taimaka wa gwamnatin jihar wajen cimma nasarorin da ta samu.

A nasa ɓangaren, Gwmana Bala ya yi wa Kakakin maraba da zuwa PDP, tare da ba shi tabbacin za su vi gaba da yin aiki tare saboda girmama jam’iyya da ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *