Kotun Ƙoli ta ɗaure John Yakubu shekara shida da tarar biliyan N22.9

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Ranar Laraba ne Kuton Ƙoli ta Nijeriya ta jaddada hukuncin ɗaurin shekaru shida da tarar kuɗi zunzurutun nairori biliyan 22.9b ga wani jami’i mai suna John Yusufu Yakubu wanda ake zargin ya sace kuɗi Naira biliyan 25 daga asusun kuɗaɗen fansho na ‘yan sanda.

Alƙalai biyar na Kotun Ƙolin duka bakunan su sun kasance bai ɗaya bisa jaddada hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja da ta yanke a shekarar 2018.

Tijjani Abubakar, wanda ya karanta hukuncin kotun ƙolin, ya amince da tarar Naira biliyan 22.9 da aka ƙara akan ɗauri da aka zartar akan mai laifin, yana cewar, ya yi daidai da nauyin aikata laifin, da kuma tasiri akan ‘yan sanda da suka yi ritaya masu jiran kuɗaɗen sallama.

“Ya zama wajibi a fayyace cewar, ‘yan sanda da suka yi ritaya suna jiran haƙƙin su, suna da ‘yancin neman diyyar wannan katoɓara da aka yi masu, a faɗin Abubakar, ya ƙara da cewar “na goyi bayan hukuncin ƙaramar kotun.”

Ya bayyana hukuncin babbar kotun ta Birnin Tarayya Abuja ta watan Janairun shekara ta 2013, wacce tun daga farko ta yanke wa ɓarawon kuɗaɗen fanshon wa’adin shekaru biyu a gidan gyara hali ko tarar kuɗi Naira 750, 000 tamfar shafar hannu.

Abubakar ya bayyana cewar, hukuncin da babbar kotun ta ƙaƙaba bai taka kara ya karya ba, kuma bai isa ambata ba.

“La’akari da maqudan kuɗaɗe da aka sace, hali da nauyin laifi da aka aikata, haɗi da ɓarnar da laifin ya jawo wa ƙasa, da kuma munmunan tasiri da yayi akan ‘yan-fansho da wulakantar da amanar aiki, matsanancin hukunci da zai rage wa hukuma jin takaicin laifin, kuma ya hana wa mai laifin samun wata riba daga abinda ya aikata”, a cewar Abubakar, yana mai ƙarfafa kalmomin kotun ɗaukaka ƙarar akan batun.

Sauran alƙalan da suka yanke wannan hukunci ƙarƙashin jagorancin Helen Ogunwumiju dukkan su sun amince da hukuncin kotun. Alƙalan sun haɗa da Musa Dattijo Muhammad, Centus Nweze da Adamu Jauro.

Abubakar ya kuma karanta ɗaiɗaikun hukuncin sauran alƙalan guda huɗu da basu samu zaman kotun ba, da hukuncin su suka yi bai ɗaya da juna a ranar ta Laraba.

Wani alƙalin kotun ƙolin, wanda kuma ya tsara hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar a shekara ta 2018 ya zauna ne a ganganiyar Abubakar.

Mista Agim ba ya cikin alƙalan kotun ƙolin da suka yanke wa Yakubu hukunci, amma ya zo ne domin karanta hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da lamarin ya jiɓanci shi.

Mal. Yakubu, tsohon jami’in hukumar fansho ta ‘yan sanda a shekarar 2013 ya amsa laifin sace waɗannan maƙudan kuɗaɗe daga asusun fansho, amma ya fice salin-alun bayan da ya biya tarar ‘yan kuɗaɗe ƙalilan na Naira 750,000 da kotu ta yanke masa.

Shi kaɗai ne daga cikin masu kariya wanda ya amsa tuhumce-tuhumce guda uku da hukumar EFCC ta zarge shi da su.

Alƙalin da ya yanke hukunci, Abubakar Talba wanda a lokacin yana alƙalin babbar kotun Birnin Tarayya ce ta Gudu dake Abuja, a hukuncin da ya yanke a ranar 28 ga watan Janairu na shekara ta 2013, ya yanke wa Mista Yakubu hukuncin ɗaurin shekaru biyu da zaɓin biyan tara ta Naira 750, 000.

Wannan hukunci ya sha suka daga wajen masu ruwa da tsaki. Hukumar gudanar da lamuran shari’a ta ƙasa, biyo bayan koke-koken jama’a sai ta dakatar da Alƙali Talban a wa’adin shekara guda.

Biyo bayan ɗaukaka ƙara bisa hukuncin hukumar EFCC, Babbar kotun ɗaukaka ƙara ta Abuja sai ta warware wancan hukunci na babbar kotu, tare da yin kwaskwarimar ɗaurin watanni shida, haɗi da hukuncin biyan tara ta Naira biliyan 22.9.