Kan yaƙi da cin hanci da rashawa muka shirya fim ɗin ‘Rumfar Mai Shayi’ – Nasir B.

Daga IBRAHIM HAMISU Kano

‘Rumfar Mai Shayi’ fim ne mai dogon zango, wato ‘series’, wanda babban kamfanin shirya finafinai da horarwa a masana’artar shirya finafinai ta Kannywood, wato ‘Moving Image Nig. Ltd., wanda Alhaji Abdulkarim Muhammad ke jagoranta. A wannan karon, filin Nishaɗi na Bleuprint Manhaja ya zanta da babban darakta kuma malamin da ya ke koyarwa a fagen shirya finafinai, sannan ya ke fitowa a matsayin Dogarin Gwamnan Alfawa a cikin fim ɗin ‘Kwana Casa’in’, Wato Nasir B. Muhammad. A zantawarsa da Wakilinmu a Kano, za ku ji manufofi da maƙasudin shirya fim ɗin ‘Rumfar Mai Shayi’. Ku biyo mu ku sha labari:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.
NASIR: Sunana Nasir B. Muhammad, Ni marubuci ne, darakta, kuma ina fitowa a fim, ina bada umurni a fim da kuma rubutu da bada umurni a diramar radiyo, daga kamfanin Moving image.

Ga mu a wurin ɗaukar shirin fim (location) na fim mai suna ‘Rumfar Mai shayi’, me fim ɗin ya ƙunsa?
‘Rumfar Mai shayi’ fim ne mai dogon zango da ake haskashi ta kafar ‘YouTube’, wato ‘Shot Film’ ne da ake yinsa a guri ɗaya, da baya wuce minti 10.

Kuma shi fim ɗin ana nuna shi ne domin jaddada diramar nan ta radiyo mai suna ‘Shugabanci’, wanda ake sanyawa a gidajen radiyoyi 9 na arewacin Nijeriya. Kuma shiri ne da MacArthur Foundation ta ke tallafa mana muke aiwatar da shi, wanda ya zuwa yanzu shekara huɗu kenan muna gabatar da shirin ‘Shugabanci’.


Babbar manufar shirin shi ne, yaqi da cin hanci da rashawa wanda mun sani ya adabbi ƙasar nan, kuma ya ke kawo mana cikas wajen samun cigaba. Kazalika mun tsara fim xin ne dukka a wuri ɗaya, wato a ‘Rumfar Mai shayi’ kamar yadda sunan ya nuna, saboda rumfar mai shayi waje ne da yake tara mutane daban-daban, kuma za ka samu ra’ayoyi mabambanta akan abinda ya shafi al’amurran yau da kullum, sai dai mun qara wata hikima inda muka ajiye mai ƙosai a gefen rumfar domin wakilci mata, don su ma a ji muryoyinsu. Sannan baya ga mai qosai da ‘yarta, to akwai wasu matan da suke taka rawa a fim ɗin.

Yayin ɗaukar shirin Rumfar Mai Shayi

Yaushe aka fara fim ɗin?
Mun fara ‘Rumfar Mai shayi’ zango na farko ne wata 3 da suka gabata, kuma har yanzu muna cigaba da haskawa duk ranar Talata a kafar sadarwa ta YouTube. Don haka yanzu zango na 2 muka ɗauka, wanda shi ne yake tafiya da gundarin labarin. Shi kuma Radiyo Dirama an fara shi ne shekara 3 da suka wuce, mun yi zango na da 1 da na 2. To haka shima ‘Rumfar Mai shayi’ mun yi na ɗaya na biyun ne muka kammala ɗauka.

A ina ake nuna fim ɗin?
Ana nuna shi ne a YouTube, kuma idan ka rubuta Moving Image/Rumfar Mai shayi za ka ga fim ɗin.

Akwai yiwuwar ku haska fim ɗin a wasu gidajen talabijin ne ko a YouTube ɗin ne kawai?
Eh duk da yake fim din ‘Rumfar mai shayi’ ƙananan bidiyo ne da bai wuce minti goma ba, to amma muna nan muna tattauna wa da wasu tashoshin talabijin, idan mun daidaita za a ji sanarwar farar haskawa.

Zaɓen 2023 yana tunkarowa. Wacce rawa kake ganin fim ɗin ‘Rumfar mai shayi’ zai taka wajen zaɓen shugabanni nagari?
Tabbas zai taka rawa, kuma dama burinmu kenan, domin idan ka duba harkar zaɓe a ƙasar nan za ka ga cewa, mutane suna yin cin dare ɗaya ne, ma’ana sai ka ga mutum an ba shi 200, ba ruwansa da ingancin sa, ba ruwansa da mai zai yi wa al’umma, wanda shi yana ganin 200 ita ce rabonsa, don haka ne muke son canza wannan tsarin, abin nufi anan, idan muka bi a hankali muka zaɓi mutane nagari, ba tare da son kansa ba ko wani mai gidansa ba, to tabbas waɗannan da suka yi wannan abin, muna kyautata zaton cewa abinda suka yi kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, to wannan haƙurin shi muke ƙoƙarin cusawa a cikin zukatan mutane.

Ta wacce hanya kake ganin za a bi don ganin an magance matsalar cin hanci da rashawa a Nijeriya?
A gani na, hanya mafi sauƙi da za a bi don ganin an magance cin hanci da rashawa ita ce, son kai; ma’ana, son kai na shi mai yin da kuma son kai na waɗanda yake bai wa toshiyar baki, saboda ko shi wanda ake bai wa toshiyar baki idan ba son ransa ba, ba zai karɓa ba, zai ga cewa hakkin al’umma ne, to amma saboda son kai ya yi katutu sai mutum ya ce shi kam ya samu na shi.

Wane albishir za ka yi wa al’umma akan wannan fim na ‘Rumfar Mai shayi’?
Albishir shi ne, al’umma su riƙa bibiyarmu don kallon wannan fim a cikin nishaɗi da isar da saƙo duk ranar Talala. Fim ɗin wanda ya zuwa yanzu an kammala ɗaukar zango na 2, wanda Nasir B. Muhammad ne Daraktan, kuma wanda ya ɗauki nauyi, sai mataimakin mai bada umurni Almustapha Adam Muhammad. Sannan sai wanda ya fito a matsayin mai shayi shi ne Abullahi Sani Abdullahi (Baba Ƙarami) wacce ta fito a matsayin mai ƙosai ita ce, Sadiya Sokoto. Marubuta fim ɗin sune; Zubairu A Kasim da Almustapha Adam Muhammad. DOP ɗin shirin ya zama Adamu Dausayi. Sai mai kula da ci gaban shiri shi ne, Abubakar Yahaya (Matinko) yayin da Jibrin Kwastum yake a matsayin mai kula da sutura.