An yanke wa matar aure hukuncin sharar kotu kwana biyar a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alƙalin Kotun Majistare, Ibrahim Emmanuel, jiya Alhamis ya umarci wata matar aure mai suna Hadiza Ahmed da ta share harabar kotun na tsawon kwanaki biyar saboda ta yi wa makwabciyar ta duka.

Emmanuel, ya bada umarnin ne biyo bayan amsa laifin da Hadiza Ahmed ɗin ta yi.

“An umarce ki da ki share tare da tsaftace harabar kotun nan na tsawon kwanaki biyar a ƙarƙashin bibiyar magatakardan kotun.

“Hukuncin zai zama izina ga wasu da ba sa son zaman lafiya da maƙwabta,” in ji shi.

Tun da fari dai, lauyan masu shigar da ƙara, Sufeto Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa Hadiza ta aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Maris a Tudun Wada, Kaduna.

Leo ya ce  ba tare da wata tsokana ba, Hadiza ta buɗe baki ta zagi mai ƙorafin, Farida Musa, inda hakan ya maishe su ga faɗa.

Ya ƙara da cewa, a yayin faɗan, wacce a ke ƙara ta lakaɗa wa mai ƙarar dukan tsiya.

Laifin, a cewar sa ya saɓa wa tanadin sashe na 173 na kundin laifuffuka na Jihar Kaduna na 2017.