Matasa ne barazanar Arewa da ‘yan Arewa a yanzu?

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Wato a yau da kuma wasu ‘yan shekaru masu zuwa, ba abinda hasashe ya nuna yane barazana ga Arewa da kuma ‘yan Arewa irin matasanta ‘yan shekara 13 zuwa 25. 

Yawancin wannan yaran ba su san inda suka dosa ba a rayuwa, ba su da manufa, kuma ba a ɗora su a kan wata hanya mai kyau ba. Hakazalika, ba ruwansu da tarbiyyar addini, ba abunda ya shafe su da tarbiyya kyakyawa ta al’ada. 

Yara ne da babban abin da suka sanya a gaba shi ne, ya za su yi kuɗi, kuma za su iya yin komai don su samu kuɗin walau ko ta haurawa gidaje su yi sata, ko ƙwacen waya a hanya, ko a masallatai, ko asibitoci ko maƙabartu, ko ma a ina ne!

Yara ne da suke neman shahara ko ta halin ƙaƙa, walau ko ta hanyar waƙar hip-hop, ko jagaliyar siyasa ko ta instagiram ko tik-tok, ko ta hanyar mammunar shiga da mugun aski irin na manyan kafirai.

Babbar alƙiblarsu ita ce Duniya! Duk inda ta nuna musu, nan suke bi. Su ba ruwansu da koyi da mutane nagari ko wasu malamai, a’a! Su fitilarsu su ne, ‘yan fim da mawaƙa, musamman wanda suke taka rawa a matsayin lalatattu a fim da masu waƙar banza!

Wasu da yawa ba sa sallah, ba ruwansu da azumi, ba ruwansu da karatu, koawanne iri ne kuwa! Za ka sha mamaki idan kana hira da su, a nan za ka gane cewar muna cikin hatsari babba. Ka ga yaro bai san bihim ba a addini, bai san komai ba a ilimin zaman duniya, bai san tarihi ba ( wani ko sunan kakansa bai sani ba) bai san komai ba sai ‘yan ƙwallo, da waƙoƙin shirme da labarin motoci! 

Ko ‘social media’ ɗin nan fa ba iyawa suka yi ba, sai jarrabar ɗaukan hoto, da shige- shigen mugayen shafuka.

Wasu yadda ake gaishe da na gaba da su ma ba su iya ba, wasu ko hira ba su iya ba, sai ɗan karen ashar!

Ya aka yi muka tsinci kanmu a haka? Ina mafita? Za mu ɗora daga inda muka tsaya, kada rubutun ya yi tsayi.

Mukhtar Mudi Sipikin matashi ne mai sharhi a kan lamurran yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *