LeBron James ya zama ɗan wasan NBA na farko da ya zura ƙwallaye 50,000

Spread the love

James ya kai maki 50,000 a kakar wasannisa 22, wanda ake alaƙanta shi da ɓince Carter na wanda ya fi zura ƙwallaye a kwando a tarihin gasar NBA.

LeBron James ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙwando ta Amurka na farko a tarihi da ya zura ƙwallaye 50,000, idan aka hada da ƙwallayen da ya ci kafin da kuma lokacin kakar wasanni a daren ranar Talata.

James ya fara da wani bugu mai kyau da ya zura ƙwallo da maki 3 a farko zagaye na farko na wasan Los Angeles Lakers da New Orleans Pelicans.

James ya samu maki 49,999 a daren ranar Lahadi da ta gabata, lokacin da ya ci ƙwallaye 17 yayin da Lakers suka doke Clippers da ci 108-102 a karo na shida a jere.

James mai shekaru 40 ya riga ya zama ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin NBA a duk lokacin kakar wasanni da wasanni share fage a lokacin da yake murza leda a lokacin da sake rubuta dukkan ma’anar da suka gabata na tarihin ƙwallon Kwando.

James ya kai maki 50,000 a kakar wasannisa 22, wanda ake alakanta shi da ɓince Carter na wanda ya fi taka leda a tarihin gasar NBA.

Shahararren ɗan wasan Lakers Kareen Abdul-Jabar, wanda ya buga kakar wasanni 20, shi ne a mataki na biyu a tarihin gasar NBA da maki 44,149.

By ukarofi