
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗan jaridar ɗaukar hoto na jaridar Blueprint mai suna Sunday Essiet ya tsinci kansa a mawuyacin hali yayin da jami’an Taskforce na kula da muhalli a Jihar Legas suka lakaɗa masa duka.
Sun kuma tsare shi na tsawon sa’o’i 10 a lokacin da yake bakin aiki.
Al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, a yankin rukunin gidaje na Jakande yayin da jami’an ke gudanar da wani aiki.
Mista Essiet ya bayyana cewa, sai da ya samu umarnin ɗaukar rahoton aikin jami’an daga wani babban jami’in ƴan sanda kafin ya fara aikin.
A yayin da aka gan shi da kyamararsa ta ɗaukar hoto ne sai ƴan sandan da wasu jami’an da ke wajen suka kama shi tare da ƙwace masa kyamarar.
A nan suka masa duka, yaga masa kaya da kuma karɓe katin shaidarsa da wurgi da shi cikin yanayi na wulaƙanci.
A cewarsa, baya ga haka ne aka ja shi zuwa wata motar ƴan sanda inda nan aka rufe shi tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa 7 na dare ba tare da ba shi abinci ba.
Bayan an kira Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Olohundare Jimoh, sai ya kira shugaban jami’an na Taskforce, CSP Adetayo Akerele, wanda ya bada umarnin a sake shi.
