NiMET ta sake hasashen mamakon ruwan sama na kwana uku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da yanayi ta ƙasa NiMET, ta ce ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama na kwanaki uku daga yau Litinin zuwa Laraba a faɗin Nijeriya.

A rahoton hasashen da ta fitar ranar Lahadi a Abuja, ta bayyana cewa ana sa ran samun hadari da tsawa a Litinin da yayyafi a wasu yankunan jihohin Adamawa da Taraba a lokacin safiya.

Ta bayyana cewa, akwai yiwuwar a samu hadari da yayyafi a Kaduna, Gombe, Kebbi, Zamfara, Adamawa, Bauchi, Kudancin Borno da Taraba daga bisani a ranar.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMET ta yi hasashen hadari da rana, inda daga bisani ake sa ran samun yayyafi a yankunan jihohin Nasarawa, Abuja da Neja.

A gefe guda kuma, hukumar ta ce ana sa ran samun rana da hadari da yayyafi a shiyyar kudu a sassan Ibonyi, Abia, Imo, Lagas, Delta, Bayelsa, Ribas, Kuros-Riba da Akwa-Ibom a lokacin safiya na ranakun.

Kazalika, ta yi hasashen yayyafi a yankunan jihohin Kaduna, Bauchi, Gombe, Borno, Adamawa da kuma Taraba a lokacin safiya a Laraba.

By Babaji