Masarautar Ƙaura Namoda ta horar da mambobin MSSN akan tsarin shugabanci a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Masarautar Ƙaura Namoda ta ɗauki nauyin horaswa ga mambobin ɗalibai musulmi na Najeriya MSSN reshen Jihar Zamfara na tsawon kwanaki domin sanin tsarin shugabanci.

Da yake jawabi yayin rufe taron bayar da horon da aka gudanar a ɗakin taro na Federal Polytechnic Ƙaura Namoda yau Lahadi, Mai Martaba Sarkin Ƙaura Namoda Alh. Sanusi Muhammad Asha yace maƙasudin bada horon shine a wayar da kan matasa kan ginshiƙin shugabanci.

Sarkin ya jaddada aniyar masarautarsa na ganin an yaɗa ilimin addinin musulunci, yana Mai nuni da cewa, masarautar sa a shirye take ta tallafa wa duk wata ƙungiya da ke son inganta ilimi.

“Masarautar tawa ta ɗauki nauyin horaswar ne domin faɗakar da matasanmu yadda za su bada gudumawa wajen ci gaban al’umma duba da cewa su ne shugabannin mu na gobe”. Yace

Basaraken yayi kira ga ɗaliban da su guji aikata duk wani nau’i rashin ɗa’a ko shiga wasu haramtattun ƙungiyoyin da ka iya kawo masu nakasu a fannin karatun su.

Da yake jawabi tun da farko shugaban majalisar sarakunan Jihar zamfara kuma mai martaba sarkin Anka Alh. Attahiru Ahmad, ya yabawa masarautar Ƙaura Namoda bisa ɗaukar nauyin taron horaswar na ƙungiyar ɗalibai Musulmi na MSSN reshen jihar.

Ya kuma umurci ‘ya’yan ƙungiyar a jihar da su ruɓanya ƙoƙarinsa wajen yaɗa zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban al’ummar musulmi.

Auwal Ahmad Shinkafi, ma’ajin ƙungiyar ta MSSN reshen Jihar Zamfara, a cikin jawabin godiya a madadin mambobin ƙungiyar, ya yabawa masarautar Ƙaura Namoda da ta dauki nauyin gudanar da wannan taro a tsakanin mambobin ƙungiyar a jihar.

A cewarsa, horarwar da aka yi a tsakanin mahalarta taron zai yi matuƙar tasiri wajen bunƙasa tarbiyyarsu a manyan makarantun su.

By ukarofi