
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin mutane 10 ne suka nutse yayin da wani kwale-kwale da ya yi jigilar fasinjoji a ranar Alhamis a Ƙaramar Hukumar Sabon Birnin da ke jihar Sakkwato ya kife a ruwa, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.
Yayin zantawarsa da manema labarai, Kakakin ƴan sandan jihar, Ahmed Rufa’i, ya ce al’amarin ya auku ne a wani ƙauye mai suna Zalla Bango, a lokacin da kwale-kwalen mai ɗauke da tarin mutane da kayayyaki ya nutse.
Ya ce, an gano baki ɗaya gawawwaki goman waɗanda galibin su yara ne.
Saidai ƴan sandan ba su san ko mutanen da iftila’in ya afka wa suna gudun wa harin ƴan bindiga ne a lokacin da abin ya faru.
Da fari, rahotanni sun bayyana cewa ƴan ƙauyen, waɗanda galibin su mata suna ta ficewa daga yankin sakamakon fargabar harin ƴan bindiga.
Haka kuma an gano cewa kwale-kwalen ya kife ne a lokacin da ya ci karo da wani kututturen magudanan ruwa a yankin hanyar Goronyo zuwa Sabon Birni.
Kakakin ƴan sandan ya kuma bayyana cewa, a wannan shekarar an samu irin hatsarin da dama a jihar Sakkwato musamman a yankunan karkara.
