’Yan bindiga sun yi garkuwa da mai taimaka wa gwamnan Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a Jihar Nasarawa, sun yi garkuwa da Dakta Muhammed Egye Osolafia, wanda shi ne mai taimaka wa Gwamna Abdullahi Sule akan harkokin jinƙai.

Al’amarin ya auku ne daren ranar Asabar wayewar Lahadi a yankin Tudun Amba da ke garin Lafiya, inda maharan suka yi ta harbe-harbe a sama tare cim masa a lokacin da ya ke ƙoƙarin shiga gidansa.

Mai ba gwamna shawara akan harkokin hulɗa da jama’a Mista Peter Ahemba ya tabbatar da faruwar al’amarin ga manema labarai a Lafiya, jiya Lahadi.

Al’amarin garkuwa da mutane a Lafiya da wasu sassan jihar ya fara zama ruwan dare, inda ƴan sanda sun kama mutane da dama da hannu a irin laifin a ƴan kwanakin nan.

A kwanan nan Gwamna Sule ya gargaɗi manyan jami’an gwamnati akan yin amfani da ƙarfi wajen sa a sako masu laifi daga hannun jami’an tsaro.

Ƙwararru akan harkokin tsaro na ganin yaɗuwar mutanen da aka ɗaiɗaita sakamakon harin ƴan bindiga daga jihohin maƙota kamar Benuwai da matsin lamba ga ƴan ta’adda daga sojoji na daga cikin ababen da suka sabbaba yawaitar garkuwa da mutane a jihar kasancewar wasu ƴan ta’adda sun mayar da ayyukansu zuwa Nasarawa.

By Babaji