
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Lahadi aka yi addu’ar uku na rasuwar marigayi Sarkin Gabas kuma Hakimin Kabo, Idris Ɗankabo a Jihar Kano.
Malam Umar Ali ne ya jagoranci addu’ar tare da wasu malamai a gidan kakan marigayin, wato marigayi Adamu Ɗankabo.
Dubunnan jama’a ne suka taru a yayin haka inda aka samu makaranta Al-Ƙur’ani mai girma suka gudanar da karatu domin roƙa wa mamacin rahamar Allah.
Daga cikin masu alfarma da suka halarci taron akwai tsohon Ministan Shari’a Bello Adoke; Gwamna Abba Kablr Yusuf na jihar Kano da mataimakinsa Aminu Gwarzo; da Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Abdul’Aziz Abdul’Aziz.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Kano,Sanata Rabiu Kwankwaso; Hamshaƙin attajiri, Aliko Ɗangote; da tsohon Kakakin Majalisar Dokoki ta Kano, Kabiru Rurum.
A ranar Alhamis Sarkin, mai shekaru 48 ya rasu a birnin Kano bayan wani hatsari ya rutsa da shi.
Haka kuma, Ɗankabo shi ne babban ɗa ga Adamu Ɗankabo, wato Jarman Kano kuma wanda ya samar da kamfanin jiragen sama na Kabo Air.
