Shiin Gaza

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Kusan watanni da dama na samarwa kaina mafita daga bakin cikin wannan yankin ta hanyar watsi da kallon abinda ke faruwa a kan falasdinawa da ke zaune a zirin Gaza, da kuma gamsuwa da gane cewa laifin ba fa na Isra’ila ba ne, ko Amurka, a’a ko kadan, laifi ne na Musulmi. Dakata, dakata… biyo ni a hankali.

Abinda ya sa na daina ganin laifin Isra’ila da Amurka a kan wannan yankin na koma kan Musulmi shine: Da farko dai kowa ya san karfin tattalin arzikin kasashen Gulf wadanda ke juya akalar cinikayyar danyen man fetur a duniya. Masu karanta tarihi kuma za su iya tuna yadda kasashen Larabawa su ka tsayar da yakin 1973 ta hanyar amfani da wannan karfin Iko na ciklnikin mai. Ta Yaya za’a ce a yanzu da kasar Saudia kadai ba tare da ragowar Yan uwanta na Gulf ba, za ta iya shake wuyan Duniya ta hanyar amfani da man ta, amma sun zuba Ido ana cin mutuncin Musulmai da Musulunci?

A kwanan baya mun ga yadda Iran cikin kwanaki 12 ta durkusar da Isra’ila har sai da su ka nemi tsagaita wuta da kansu, amma Iran ta koma ta nade hannunta ta na kallon yadda ake wa falasdinawa a Gaza.

Mu na ganin yadda kasashen China da wasu mutane yankin turawa ke fitowa karara su na taimakon falasdinawa da kuma har kasashen yammacin Turai irin su Ireland, France da sauransu da ke ayyana goyon bayan kasar Falasdinu. Amma abin kunya Kasashen Gulf sun tattarawa Trump tiriliyan kusan shida kuma su na yi masa sujada sannan sun kasa tsayar da zaluncin da ke faruwa a Gaza.

To, a yanzu dai abinda na fahimta bayan wannan hari na baya bayan nan da Isra’ila ta kaiwa shugabannin Hamas a Doha, alamu sun nuna cewa ba kawai sadaukar da Hamas Yan uwanta na yankin Gulf su ka yi ba, har ma siyar da Gaza ga Trump da Isra’ila su saka hannunsu a ciki.

Karkashin wannan tsari da ake ganin kamar almara ne, Trump ya shirya ganin cewa bayan Isra’ila ta gama ruguje Gaza (yanzu dama kusan kaso 80% a ruguje ya ke) Attajiran yamma irinsu Trump da abokanensu za su dauko jari su sake gina Gaza a matsayin wani wajen shakatawa ga attajiran turawa, Larabawa da Isra’ilawa.

Yin wannan resort na Gaza, zai kawar wa Isra’ila da tsoron abokan gaba a kusa, ya raba Larabawa da matsalar Gaza, ya baiwa Amurkawa miliyoyin daloli. To hakika hakan solution ne na gajeren zango ga Isra’ila, Amurka da kasashen Gulf, domin dai rushe Gaza ba shi ne rushe falasdinawa ba, kuma ba shine rushe Hamas ba ko akidar kin jinin Isra’ila. A takaice ma, wannan tsari shine zai sa gaba da tsana da kiyayya su ci gaba da ruruwa tsakanin al’ummar Yahudawa da Falasdinawa, wadda zalunci da yake-yake na sama da shekaru kusan 3000 ba canza komai ba. Mu je zuwa….

By ukarofi