Likitoci na kula da halin Dharmendra, ku sanya shi a addu’a, inji matarsa Hema

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A halin yanzu daɗaɗɗen jarumi kuma tsohon ɗan siyasar ƙasar Indiya, Dharmendra yana kwance a gadon asibiti a birnin Mumbai inda likitoci ke cigaba da kula da shi

Matarsa Hema Malini, wadda ita ma sananniyar jaruma ce tun tsawo shekaru 50 da suka gabata a masana’antar Bollywood, ta sanar da haka a jiya Litinin.

Ta yi godiya ga ɗaukacin jama’a da suke cigaba da nuna damuwa akan halin da yake ciki inda ta yi magiyar da a sanya shi acikin addu’o’in fatan samun waraka, kamar yadda ta wallafa ta kafar X.

Jarumi Dharmendra mai shekaru 89 a duniya ya shafe tsawon kwanaki kwance a asibiti.

Wata majiya daga masana’anta ta ce al’amarin rashin lafiyar nasa ya yi ƙamari, amma likitoci na iya bakin ƙoƙarinsu.

Wakilan ɗan jarumin, wanda shi ma sanannen jarumi ne, wato Sunny Deol sun musanta rahotannin da cewa tauraron na fim ɗin ‘Sholay’ yana halin fafutukar numfashi.

Sannan, Hema Malini, Sunny Deol da ƴar Dharmendran, Esha Deol sun ziyarci asibitin domin kula da shi.

Haka kuma, jarumi Salman Khan ya ziyarce su a asibitin.

By Babaji