Matar Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari sun sanar da rasuwar matarsa da ta rage, wato Hajiya Saratu Shagari bayan shafe shekaru 89 a duniya.

A wata takarda da babban ɗan tsohon shugaban ƙasar kuma Sarkin Mafaran Shagari, Kyaftin Bala Shagari ya fitar, iyalan sun ce Hajiya Saratu ta rasu ne a jiya Litinin da misalin ƙarfe 3 na yamma bayan fama da wani dogon rashin lafiya.

Ya ce, ta rayu cikin mutunci, haƙuri da sadaukarwa acikin iyalanta, wanda hakan ya sa za a yi kewar ta.

Ya kuma ce, za a yi jana’izarta a yau Talata da zarar an kammala sallar Azahar a gidansu da ke Shagari a jihar Sakkwato kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Marigayiyar ta rayu da ƴaƴa da dama, jikoki da tattaɓa kunne.

Shehu Shagari shi ne farkon shugaban mulkin farar hula a Nijeriya inda ya jagoranci ƙasar daga shekerar 1979 zuwa 1983 kafin aka hamɓarar da shi bayan juyin mulkin soji.

Ya rasu a watan Disambar 2018 bayan shafe shekaru casa’in da ɗoriya a duniya.

By Babaji