Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Dubban mabiya addinin Musulunci da Kiristoci sun gudanar da taron addu’o’i domin samun zaman lafiya da kuma tsaro a jihar Kebbi da kuma ƙasa baki ɗaya.
Taron haɗin gwiwar wanda aka gudanar a masaukin shugaban ƙasa da ke garin Birnin Kebbi ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Malam Nasir Idris ya bayar da ƙarfi ne wajen nemo hanyoyin da za a bi don daƙile matsalar tsaro da sauran ayyukan ta’addanci, inda gwaman ya buƙaci jagororin addinan da su duƙufa wajen wayar da kan mabiyan su kan muhimmancin zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa babu jiha ɗaya a ƙasar nan da ke zaune lafiya, kowace jiha tana da nata irin matsalar da ta addabe ta, a Kebbi musulmi da Kiristoci da ƙabilu daban-daban duk ana zaune tare lafiya, wannan shi ma kan sa wani abin alfahari ne.
Ya kuma nemi sauran jihohin ƙasar nan da su yi koyi da jihar Kebbi wajen haɗin gwiwa tsakanin mabiya mabambantan addinai da sarakunan gargajiya wanda yin haka zai kawo samun nasara wajen samun zaman lafiya da daƙile ayyukan ta’addanci.
Ya kuma nuna jin daɗin ganin yadda Musulmai da Kiristoci suka dunƙule waje ɗaya don nemo bakin zaren matsalar tsaro inda ya kuma nemi su cigaba da baiwa wannan gwamnatin haɗin kai.
Shehin Malamin addinin musulunci, Malam Abbas Jega ya danganta rashin tsaro da fitine-fitinen da ke faruwa a Najeriya da yawan saɓon Allah da ‘yan ƙasar ke aikatawa. Ya hori jama’a da, “Ku daina aikata dukkan laifika, kamar ƙarya, zamba, cin amana, saɓa alkawari,kashe-kashe, tsafe-tsafe, fashi da makami da sace-sacen da ake yi a ruwa da tudu”
