Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta janye yajin aikin da take gudanarwa tare da ba da tabbacin mambobinta za su koma bakin aiki a wannan Asabar ɗin.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Orji ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.
“…mun janye yajin aiki. Za a ci gaba da aiki gobe (Asabar) da ƙarfe 8 na safe. Za mu waiwayi matsayar da aka cim ma nan da makonni biyu,” in ji Orji a cikin wani gajeren saƙo da ya aike wa jaridar News Point Nigeria.
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da likitocin suka dakatar da aniyarsu ta gudanar da zanga-zangar gama-gari don neman biyan buƙatunsu a wajen gwamnati.
NARD ta ce likitocin na ƙoƙarin cim ma buƙatunsu ne a wajen gwamnati da suka haɗa da ɗaukar ƙarin likitoci don cike giɓin da ake da shi sakamakon tafiya aiki a ƙetare da wasunsu suka yi da dai sauransu.
Tun a ranar 25 ga Yulin 2023 liktocisuka fara yajin aiki lamarin da ya jefa fannin lafiyar cikin wani mawuyacin hali.