Yaƙi na shirin ɓarkewa tsakanin ECOWAS da Nijar

*Ƙungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta su yi shirin ko-ta-kwana
*Tinubu ya aike da malaman Musulunci Nijar don shiga tsakani
*Mu na bin Nijar bashin Naira Biliyan huɗu na lantarki, inji Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daga dukkan alamu matuƙar al’amura ba su sauya ba, yaƙi yana shirin varkewa tsakanin Ƙungiyar Tattalin Arziki ta Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ƙarƙashin jagorancin Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da sojojin da suke riqe da madafun iko a Ƙasar Nijar bayan sun kifar da halastacciyar gwamnatin dimukraɗiyya a ƙarƙashin jagorancin Mohamed Bazoum, wanda sojojin suka hamɓarar.

Hakan ya biyo bayan yadda shugabannin Ƙasashen ECOWAS suka bayar da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar tasu ne kan su ɗaura ɗamarar kai hari Nijar a kowane lokaci daga yanzu.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, Shugaban Hukumar ECOWAS, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun bayar da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na ECOWAS da yiwuwar tilasta aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen a kan Nijar.

Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Cikin sauqi, ba za a iya fayyacewa qarara, a kan ko umarnin yana nufin dakarun sojin ECOWAS za su auka wa Nijar da yaƙi, ko kuma za su ɗaura ɗamara su zauna cikin shirin yaƙi ba.

Tun da farko, ECOWAS ta bai sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.

Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron ECOWAS suka bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.

Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.

Ƙungiyar ta ce za ta tabbatar da ganin ana aiki da duk ƙudurorinta kuma har yanzu duk ƙofofi a buɗe suke. Shugabannin sun kuma ɗora wa jagororin ECOWAS alhakin ci gaba da bibiyar takunkuman da aka ƙaƙaba wa shugabannin juyin mulki a Nijar.

Haka zalika, sun gargaɗi waɗanda suka ce suna kawo cikas ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Nijar su guji yin haka.

Tinubu ya tura malaman addini su yi aikin jakadanci:

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bai wa ƙungiyar malaman addinin Musulunci izinin ganawa da gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar a wani yunƙuri na warware rikicin zamantakewa da siyasa a ƙasar.

Malaman addinin waɗanda suka bayyana hakan a lokacin da suke zantawa da manema labarai bayan ganawar da suka yi da shugaban ƙasar, sun ce shugaban ya amince da tayin nasu.

Malaman ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar Jama’a tul Izalatul Bid’ah wa Iƙamatus Sunnah ta Ƙasa, Sheikh Bala Lau, sun shawarci shugaban na Nijeriya kan amfani da ƙarfi a Nijar.

“Muna son samun mafita mai ɗorewa. Muna son zaman lafiya ta tabbata, ba a Nijeriya kaɗai ba har ma a yankin Kudu da hamadar Sahara da ma duniya baki ɗaya.

“Don haka, dukkan Malamai suka shawarci Shugaban Ƙasa, cewa muna son zaman lafiya da sulhu,” Sheikh Lau ya shaida wa manema labarai bayan ganawar da shugaban na Nijeriya.

Shi ma da yake jawabi, shugaban ƙungiyar Ansarudeen Society of Nigeria, Sheikh Abdurrahman Ahmad, ya ce Mista Tinubu ya yi alqƙawarin cewa “idan kuma za mu iya yin magana da jama’ar da ke gefe, don su kasance a shirye su ba da rangwame, sannan ECOWAS, cewa ya yi shi kuma shugaban ƙungiyar a shirye yake.

“Shugaban kamar yadda ya ce ya yi maraba da shiga tsakani da muka yi, kuma ya yi alƙawarin cewa idan har za mu iya yin magana da mutanen da ke gefe domin su kasance a shirye su ba da rangwame, to ita ma ƙungiyar ECOWAS da yake shugabanta za ta shirya.

“Bayan haka, shugaban ya nuna rashin amincewa da juyin mulkin da aka yi a yankin Sahel kuma a matsayinsa na mai bin dimokraɗiyya ya ce zai yi duk abin da zai tabbatar da cewa an samu dimokuraɗiyya, adalci, ‘yanci da zaman lafiya a yankin,” inji Sheikh Ahmad. 

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya kuma Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi, ya gana da waɗanda suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Sanusi, wanda ya ziyarci Shugaba Tinubu a ranar Laraba domin yi masa bayani kan yunƙurin sasanci da ya ke yi a maƙwabciyar ƙasar, ya ce ya ɗauki matakin ne domin ganawa da gwamnatin mulkin soji don karan kansa.

Bashin Nijeriya ya yi wa Nijar katutu:

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta ce a halin yanzu Jamhuriyar Nijar na bin Nijeriya bashin N4.22bn ($5.48m) na samar da wutar lantarki.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin rahoton kwata na farko na NERC da aka fitar a ranar Laraba, 9 ga Agusta, 2023.

A cewar rahoton, kamfanin samar da wutar lantarki na Nijeriya, Nigerien Electricity Society, har yanzu bai aika da Dala miliyan 5.48 da kamfanin samar da wutar lantarkin na kasuwar Nijeriya ya bayar ba.

“Babu ɗaya daga cikin abokan cinikin ƙasa da ƙasa da ya yi wani biya a kan adadin dala miliyan 16.11 da aka ba su a shekarar 2023/Q1; Paras-SBEE (Dala 3.46m), Transcorp-SBEE (Dala 3.85 miliyan), Mainstream-NIGELEC (Dala 5.48m) da Odukpani-CEET (Dala 3.32 miliyan).

“Daga cikin daftari N842.38m da MO ya bayar ga dukkan abokan hulɗa guda takwas na NESI, North-South/Star Pipe ne kawai ya aika da N15.38m akan takardar sa na N24.69m,” inji ta.

A shekarar 2022, kashi 70 na kason wutar lantarkin Nijar an sayo su ne daga babban kasuwancin Nijeriya, a cewar wani rahoto da NIGELEC, mai samar da wutar lantarki tilo a ƙasar.

Dam ɗin Kainji da ke jihar Neja ne ke samar da wutar lantarki da ake kaiwa Nijar.

Nijar na ƙoƙarin kammala madatsar ruwanta na farko nan da shekarar 2025 domin karya dogaro da makamashin da ta ke yi ga Nijeriya.

An bayar da rahoton cewa, dala miliyan 5.48 na samar da wutar lantarki da kamfanin samar da wutar lantarkin na Nijeriya ya bayar, an ce ba a biya shi daga kamfanin wutar lantarki na ƙasar Nijar ba.

A halin da ake ciki, NERC ta umurci Ma’aikacin Kasuwa da ya yi amfani da wannan magana a cikin ƙa’idojin kasuwar don dakatar da rashin ɗa’a na biyan ‘yan kasuwar daban-daban.

A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, wanda ya ruwaito majiyoyin masana’antu na cikin gida, ya ce Nijeriya ta katse layin wutar lantarki mai ƙarfin gaske dake jigilar wutar lantarki zuwa Nijar tun ranar Talatar makon jiya.

Kimanin sa’a  aya a jere, mazauna Yamai, Maraɗi, da Zinder sun samu wutar lantarki kafin a rufe shi na tsawon sa’o’i biyar. A jamhuriyar Nijar, inda ake yawan samun kayyayaki da kuma abin dogaro, rashin wutar lantarki irin waɗannan ba kasafai ba ne.

Kunle Olubiyo, kodinetan sashen kula da wutar lantarki kuma shugaban ƙungiyar kare haƙƙin masu amfani da wutar lantarki ta Nijeriya, ya tabbatar da cewa ƙungiyar ECOWAS za ta katse hanyoyin samar da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar.

“Kusan kashi 60 cikin 100 na wutar lantarkin da ake bai wa Nijar daga Nijeriya ne. Kamar dai yadda ƙungiyoyin ƙwadago ke rufe hanyoyin samar da wutar lantarki na ƙasa a zaman wani ɓangare na tattaunawa lokacin da duk wani kiraye-kirayen ya kasa cimma nasara, Mista Tinubu shi ne Shugaban ECOWAS a halin yanzu.

Dam ɗin Kandadji, wanda ke da nisan kilomita 180 daga saman Yamai, ana sa ran zai samar da makamashin awoyi gigawatt 629 a duk shekara.​