Ma’aikata a kama sana’a, cewar Gwamna Matawalle

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya yi kira ga ma’aikatan gwamnatin jihar cewa baya ga albashi da suke karɓa duk wata, akwai buƙatar su duba su haɗa da sana’a domin samun ƙarin kuɗaden shiga saboda a cewarsa, gwamnati ba ta da halin biyan  sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan ya ce a halin da ake ciki, gwamnati na fama da biyan basussukan da ta gada daga gwamnatin da ta gabace ta na biyan albashi da gudanar da harkokin gwamnati.

Matawalle ya bayyana hakan ne a Juma’ar da ta gabata sa’ilin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) don su yi buɗe-baki tare a gidansa da ke Gusau.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Afrilun 2019 ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar sabon albashi mafi ƙarancin hannu. Dokar ta nuna an ƙara mafi ƙarancin albashin da ma’aikatan gwamnati ke samu daga N18,500 zuwa N30,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙarancin a Nijeriya.

A cewarsa, “Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da ke samun kaso mafi ƙanƙanta daga baitul mali duk wata, kuma ana cire mata sama da Naira bilyan N1.6 duk wata matsayin biyan bashin da ta gada daga gwamnatin da ta gabace ta.

“Abin da kan rage ma jihar duk wata bayan zabtare basussukan da ake bin ta, shi ne tsakanin bilyan N1.8 da bilyan N1.3 don biyan albashin sama da ma’aikata 28,000 da kuma gudanar da sauran ayyukan gwamnati.”

Sai dai ya ce ba makawa zai biya sabon mafi ƙarancin albashin da zarar gwamnatin jihar ta samu daidaito, sannan ya yi kira ga ma’aikata da su fahimci halin da gwamnati ke ciki.

Kazalika, ya yi kira ga ma’aikatan da su duba su assasa sana”o’i waɗanda za su taimaka musu idan sun yi murabus daga aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *