Buhari ya taya Mohammed Idris murnar cika shekara 55 da haihuwa

Daga BASHIR ISAH

A yau ne fitaccen nan a harkar yaɗa labarai, wato Alhaji Mohammed Idris, ya cika shekara 55 da haihuwa. Tuni dai dangi, ‘yan’uwa da abokan arziki suka shiga zazzaga wa jigon fatan alheri dangane da zagayowar wannan rana mai muhimmanci a rayuwar Kakakin Nupe.

Shi ma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bai bari an baro shi baya ba, domin kuwa ya aike da saƙonsa na taya murna ga Babban Sakataren Ƙungiyar Masu Jaridu na Nijeriya (NPAN), Alhaji Mohammed Idris, bisa cikarsa shekara 55 da haihuwa.

A cewar Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Garba Shehu, “Shugaba Buhari ya yi taya murna ga Idris, Kakakin Nupe, Shugaban Kamfanin Bifocal, mamallakin tashar WEFM 106.3, kuma mawallafin jaridun Manhaja da Blueprint tare da jinjina masa dangane da zuba jari da ya yi a masana’antar yaɗa labarai ta Nijeriya wanda a kowane lokaci yake aiki bisa adalci.”

Kazalika, Shugaban ya yaba da ƙoƙarin Babban Sakataren NPAN ɗin wajen yin gaba-gaba a harkar ɗaukowa da yaɗa labarai a ƙasa ta hanyar amfani da harsunan gida wanda hakan ke taimakwa wajen wayar da kan ‘yan ƙasa , tare da kafa gidauniyar da takan bai wa marasa galihu kulawa a cikin al’umma.

A cewar Shehe, “Baya ga zuba jari a harkar sadarwa da yaɗa labarai, Shugaban Ƙasa ya yaba da ƙoƙarin Shugaban Kamfanin Bifocal wajen bada gudunmawarsa ga bunƙasa sauran fannoni da suka haɗa da yawon shaƙatawa, gine-gine, siyasa da sauransu, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa buɗi, tsawon rayuwa da kuma lafiya mai inganci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *