‘Yan bindiga sun hallaka kwamishina a Kogi

Spread the love

Daga AISHA ASAS

‘Yan bindiga a jihar Kogi, sun kashe Kwamishinan Fansho na jihar, Solomon Adebayo, a kan babbar hanyar Kabba zuwa Ilori da ke jihar.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna lamarin ya auku ne cikin daren Asabar da ta gabata sa’ilin da Marigayin ke kan hanyarsa ta zuwa yankin Kabba daga Ilori.

Majiyar Manhaja ta ce ‘yan bindigar sun buɗe wa motar kwamishinan wuta ne wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take, tare da raunata direbansa.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Da yake magana a kan batun, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, William Ayah, ya ce ‘yan bindigar sun buɗe wuta ne a kan motar Mr Adebayo inda rai ya yi halinsa nan take sannan suka jikkata direbansa.

‘Yan sanda sun ce za a gudanar da bincike kan lamarin domin zaƙulowa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a harin.

By Editor