Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ofisoshin jakadancin Nijeriya a ƙasashen ƙetare na fuskantar matsalar kuɗi, inda aka gaza biyan albashin ma’aikata, alawus-alawus, da hayar ofisoshi tsawon watanni ba.
Jaridar Newspoint ta ruwauto cewa, Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin ɗin da ta gabata, inda ta danganta matasalar da ƙarancin kasafin kuɗi da ake ci gaba da yi da kuma tasirin sauye-sauyen manufofin musayar kuɗaɗen waje.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Kimiebi Ebienfa ya sanyawa hannu, ma’aikatar ta amince da cewa lamarin ya kawo cikas ga ayyuka da dama, wanda hakan ya sa suka kasa cika muhimman haƙƙoƙin ma’aikatansu da masu hidima.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ma’aikatar ba ta da masaniya game da takunkumin da gazawar kuɗi ta sanya kan gudanar da ayyuka, waɗanda suka haɗa da rashin iya biyan albashin ma’aikatan da ake ɗauka a cikin gida, wajibcin kuɗi ga masu ba da ayyuka da hayar masu gidaje, da kuma alawus ɗin hidimar ƙasashen waje ga jami’an gida,” inji sanarwar.
Ma’aikatar ta jaddada cewa, ma’aikatan diflomasiyya na Nijeriya a ƙasashen waje ba su tsira daga yanayin tattalin arziki na cikin gida ba, tare da nuna cewa rashin isassun kuɗaɗe na tsawon shekaru ya raunana ƙarfinsu na gudanar da muhimman ayyuka kamar diflomasiyya na ƙasa da ƙasa, ayyukan ofishin jakadancin, da kare lafiyar ‘yan ƙasa.
Duk da mummunan halin da ake ciki, Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa jin daɗin jami’an hidimar ƙasashen waje da iyalansu shi ne babban abin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa a gaba.
A cewar ma’aikatar, an riga an fitar da wasu kuɗaɗe na musamman domin sauƙaƙa wannan nauyi. Ya bayyana cewa sama da kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen da ake da su an fitar da su ne, inda aka ba da fifiko wajen biyan ma’aikata, albashin ma’aikatan gida, da bashin da jami’an ke bi.
Gwamnatin ta kuma danganta wani ɓangare na matsalar da taɓarɓarewar canjin kuɗi sakamakon sauye-sauyen kuɗaɗen da ake yi.
