Daga MAHD MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da ɗirga-zirgar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC’s) na iya samun cikas wajen tara kuɗaɗen shigar da ya kai biliyan N4.8 da ta samu a farkon shekarar 2024, sakamakon dakatar da zirga-zirgar jirgin Abuja-Kaduna da Warri-Itakpe.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa, yawan jigilar fasinjojin ne ya kai kaso mafi tsoka na Naira Biliyan 4.8 da hukumar NRC ta samu a bara.
Sai dai kawo cikas a baya-bayan nan ya sa hukumar ke gudanar da aikin layin Legas-Ibadan kawai.
An dakatar da layin Abuja zuwa Kaduna ne bayan wata matsala da ta samu fasinjoji da dama, yayin da hukumar ta Warri-Itakpe ba ta ci gaba da aiki ba tun bayan dakatarwar da aka yi na biyu a ranar 17 ga Yuli, 2025, biyo bayan dakatarwar da aka yi a watan Afrilu.
Da yake magana kan illar tarzomar, tsohon shugaban Cibiyar Injiniyoyi ta Najeriya, Engr. ɓictor Oyenuga, ya ce babu shakka dakatarwar za ta shafi kuɗaɗen shiga na NRC.
“Eh, dakatarwar za ta shafi ayyukan ta fuskar kuɗaɗen shiga, amma abin da ya kamata a sa gaba shi ne gyara al’amuran da suka haifar da koma bayan.
“Tsarin jiragen ƙasa sun canja hanyar tafiya tsakanin Abuja da Kaduna.
Manajan Darakta na NRC, Kayode Opeifa, ya kuma yarda cewa kuɗaɗen da hukumar ke samu zai yi tasiri, amma ya jaddada cewa nan da nan an mayar da hankali wajen farfaɗo da jigilar da aka dakatar sakamakon haɗarin jirgin Abuja-Kaduna.
