Ya soka wa budurwarsa wuƙa har lahira

Spread the love

Wani mutum ya kashe budurwarsa mai suna Ima da wuƙa a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas.

Mutumin, wanda ake wa lakabi da Doctor ya daɓa wa budurwar tasa mai suna Ima wuƙa ne bisa zargin tana cin amanarsa.

Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a unguwar suka ce ya samo asali ne daga zargin da Doctor ke yi wa Ima, wanda ya rikiɗe zuwa tashin hankali.

Mai kula da gidan da lamarin ya faru ya kai rahoto ofishin’yan sanda na Azikiwe Division, Mile 2 Diobu, wanda hakan ya kai ga cafke wanda ake zargi.

Rahotanni sun nuna cewa an kai gawar zuwa wani gidan ajiyar gawa da ba a bayyana ba a Fatakwal.

Prince Wiro, Shugaban ƙungiyar Kare Haƙƙin ɗan Adam da Inganta Gaskiya, ya buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi da adalci.

Ya ce, “Mun ga yadda aka dauke gawar zuwa gidan ajiyar gawa yayin da ake tsare wanda ake zargi. Muna kira ga ’yan sanda da su gudanar da bincike mai adalci domin tabbatar da gaskiya.”

Ya kuma shawarci matasa da su guji dangantaka mai cike da tashin hankali: “Ba a buƙatar mutum ya zauna cikin dangantaka mai cutarwa. Rayuwarka ta fi kowace dangantaka muhimmanci.”

Kakakin ’yan sanda na Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ba ta amsa kiran waya ko saƙon da aka tura mata dangane da lamarin ba.

By ukarofi