Wata mata ’yar ƙasar Sin mai shekara 22 da haihuwa da ke fama da matsanancin tari ta girgiza da sanin cewa tana da wani ƙashin kaza a maƙale a cikin huhunta tsawon shekaru.
Bayan shekara 14 ana dubawa da kuma ɗaukar hoto don gano abin da ke haifar ma ta da tari, matar da ba a bayyana sunanta ba daga ƙasar Sin kwanan nan ta fahimci cewa duk ƙashin kaji ne ya haddasa ma ta haka.
Matsalolin matar sun fara ne bayan ta yi fama da tsananin tari lokacin da take ’yar shekara bakwai ko takwas, kuma duk da yawan ziyartar asibiti, babu wanda ya gano lamuran da ke haifar da yawan tarin.
Ba ta yarda da tari da matsalar numfashi a matsayin wani ɓangare na rayuwarta ta yau da kullum ba, matar ta ci gaba da neman taimakon asibiti, kuma an yi ma ta rashin fahimta sau da yawa a yin hakan, gami da cutar ta ‘bronchiectasis’, yanayin da ke tattare da tari mai ɗauke da danshi sakamakon lahanin hanyoyin iska da suka lalace.
Abun takaici, bayan kwashe shekaru tana shan maganin kashe kwayoyin cuta don magance cutar, yanayinta ya ƙara taɓarɓarewa. Kamar yadda rabo zai kasance, daga ƙarshe matar zata gano dalilin tari mai tarin yawa kwatsam. Ta yanke shawarar yin tiyata ne saboda cutar ‘hyperhidrosis’ (zufa mai zafi), amma likitoci sun yi wasu gwaje-gwaje don tabbatar da lafiyarta kafin ayi mata aikin, wanda a wannan lokacin ne matsalolin numfashinta suka fito, don haka, Wang Jiyong, mataimakin Shugaban Kula da tiyatar ‘Cardiothoracic’ a Asibitin First Affiliated Hospital na jami’ar Guangzhou na magungunan Sin, ya ba da umarnin saitin wani nau’in sikanin na CT.
Oddity Central ta ruwaito cewa, sikanin ɗin ya bayyana abin da ya yi kama da wani baƙon abu da aka ajiye a huhun majinyaciyar na dama, don haka likita Yang Ming ya yanke shawarar yin gwajin ‘bronchoscopy’ don gano shi.
Gwajin ‘bronchoscopy’ da ke ɗaukar minti 30, an aiwatar da shi ne da wani bututu tare da haske a gaban bututun da ƙaramar kyamara a ƙarshen da ake sakawa ta bakin mutum, zuwa ta hanyoyin iska har zuwa huhu.
Likitan ya sami nasarar gano abu mai ban al’ajabi a cikin huhun matar, ta hanyar amfani da ‘bronchoscopy’. Abin ya kasance wani yanki ne na ƙashin kaza kimanin tsawon mita 2.
Da jin labarin, mara lafiyar da ta gigice ta gaya wa likitoci cewa ba ta san yadda ƙashin ya ƙare a huhunta ba. Amma likitoci sun ce wata ƙila ta haƙiye ne bata sani ba, lokacin da take yarinya, wanda hakan ne ya haifar ma ta da duk waɗannan tarin.
