Daga MUHAMMED BALA GARBA
Sara wani irin salo ne na magana da ke ƙunshe da ƙirƙirarrun zantuka waɗanda kan yi tashe ko yayi a wani lokaci. Waɗannan zantuka sukan ba da ma’ana ta musamman ga wanda ya san su. Wani lokaci yayin wata sara yakan wuce, sai wani sabo ya shigo. Wani lokacin kuma akan samu Sarar da kan jima ba a manta da ita ba, ko da kuwa an samu wata sabuwa ta zo a bayanta. Haka nan kuma, sara na iya nufin wani yayi ko salo na yin magana da abokai ke yi a tsakaninsu wanda ya gama gari. Sara ta fi cin kasuwarta a tsakanin matasa kuma takan shafi salon magana ce ko tufafi ko kuma yanayin tafiya da dai sauransu.
MISALAI
Ga wasu Sara da misalansu ko dalilin yin su wanda Malam Fatuhu Mustapha ya yi mini bayani. Ga su kamar haka:
1. Bula ce ! Zargina ce
2. Sabuwa ce!
3. Oga at the top
4. Wai ma!
5. Ale
1. “A lokacin sarar Bula ce, in mutum ya ci kwalliya, sai a ringa tsokanar sa ana cewa “Bula ce, zargina ce”. Wato wai ba sabbin kaya ba ne, wanki ne kawai. Anyi wannan sarar a 80s.”
2. “Sabuwa ce! Ita ma wannan 70s zuwa 80s aka yi sarar, in ka hau mota tsohuwa, sai a ringa ma shegantaka da “sabuwa ce”. In kuma gudu ka ke da mota ko kana bata wuta, sai ka ji ana cewa “ci ubanta, taka ce aka baka.”
3. “Ale wata sara ce da Kanawa yan bakin kasuwa suka yi, maimakon a cewa mutum Alhaji, sai a ce masa Ale. Kamar takaita kalmar Alhaji ce.
4. “Hira aka yi da mai magana da yawun civil defence a NTA, komai aka tambaye shi sai ya ce ba zai ce komai ba sai ya samu izini daga Oga at the top.
5. “Wai ma wata sara ce da yan mata suka yi. In ka yi magana, in ba su yadda ba, sai su ce maka “wai ma.”