Mace mai sana’a ta fi daraja a idon mijinta – Balaraba Abdullah

“Ya kamata ‘yan siyasa su taimaka wa mata wajen cikar burinsu”

Daga UMAR AƘILU MAJERI 

Hajiya Balaraba Abdullahi shahararriyar ‘yar kasuwa ce da ta yi shihura wajen taimakawa mata da ƙananan yara, ita ce mace ta farko a Jihar Jigawa da ta zaɓi ta yi kasuwanci bayan ta kammala karatun ta na zamani. Ba ta sha’awar aikin gwamnati, amma Hajiya Balaraba ta yi fice a fagen siyasa har ta tava riƙe muƙamin shugabar jam’iyya ta mata wato ‘women leader’ ta jam’iyyar SDP a nan Jihar Jigawa. Yanzu haka Hajiya Balaraba ta kafa gidauniya domin taimaka wa marayu da koya wa mata sana’a domin su zama masu dogaro da kansu. Ta kuma riƙe muƙamin shugabar mata ta ‘Nigeria League of Women Voters’, kuma shugaba ta ‘Jigawa Women Consultative Forum’, Kuma shugaba ta ‘Stand up for Women Society’. Har ila yau, ita ce mataimakiyar shugaba ta ‘Northern Women in Politics’ ta kuma taɓa riƙe matsayin CEO ta ‘Ayman Global Trade Limited’. Wakilinmu na Jihar Jigawa, ya samu damar zantawa da Hajiya Balaraba a gidanta da ke unguwar Fatara, inda har ma ta yi ma sa qarin haske a kan yadda kasuwanci ya ke a Kwatano, da yadda a ke zaman amana tsakaninsu da ‘yan kasuwar Nijeriya da suke zuwa can don sayayyar kaya. Ku biyo mu, don jin yadda tattaunawar ta kasance:

Mu fara da jin tarihinki a taƙaice.

An haife ni a garin Ringim, a masarautar Ringim da ke qaramar Hukumar Ringim. Na yi karance-karance ma su tarin yawa har zuwa matakin digiri. Na kasance ‘yar siyasa, kuma ‘yar kasuwa. Babu irin abinda ba na saya na sayar, wannan ce ta sa a ke min laƙabi da ‘jack of all trade’. Hakazalika ina yin aiki da ƙungiyoyi, kuma a cikin harkar kasuwancin da na ke yi akwai harkar kayan ‘kictchen’, ina yin ‘order’ daga waje, domin sayarwa mata ‘yan ƙwalisa ko ‘ya’yan masu kuɗi ko matansu.

Ya batun iyali fa?
Ina da aure, kuma ina da ‘ya’ya uku, dukkansu maza ne. 

Mene ne burinki a rayuwa?
Babban burina a rayuwa ina son na zama babbar ‘yar kasuwa, domin ni ba ni da buri na zama ma’aikaciyar gwamnati. Amma ina da buqatar na ga ina taimaka wa jama’a. ba na son na ga jama’a a cikin halin qunci, musamman ma mata ‘yan’uwana. Ina sha’awar ganinsu cikin walwala.

Kin kasance ɗaya daga cikin mata ‘yan siyasa. Ko zamu iya sanin jam’iyyar da ki ka yi, ko ince ki ke ciki? 
A baya ina cikin jam’iyyar PDP, kuma na jima a ciki, domin sai da na kai matakin Shugabar mata ta jam’iyyar ta ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Daga baya na koma jam’iyyar SDP maidoki a wancan lokacin kenan, domin yanzu sun yi maja ita da PDP, sun zama abu ɗaya.
 
Bari mu taɓo ɓangaren tafiye-tafiye. Ko ƙasashe nawa kika taɓa zuwa?
Da ya ke ina da aure, kuma yanzu komai an samu sauƙi, za ka iya yin odar kaya kana ɗakinka, kuma a kawoma har gida. Babu wata ƙasa da na ke zuwa ban da Kwatano domin su Kwatano suna da kayan ado na kwalliya.

Ɓangaren tsadar rayuwa, ko Kwatano na cikin jerin ƙasashen da kaya suka yi tsada?
Kwatano ba su da tsada, domin sun fi mu sauƙin kaya. Kuma suna da amana, ba sa cutar da baqo, ta fuskar tsaro kuwa, zai yi wahala ka ji an ma wani fashi ko ƙwace, ba ka ganin wannan sai ka tsallako Nijeriya. Idan ka shigo Ƙasar Nijeriya ne za ka ga ababen ban takaici ta ɓangaren tsaro, amma gaskiya su a can ba su da matsalar.
 
Ya batun yanayin abincinsu. Shin akwai bambanci da na nan gida Nijeriya?
Abincinsu yana da ɗan bambanci kaɗan. Duk da akwai Yarabawa akwai Hausawa, kuma Yarabawan can ba su da wani bambanci da na Legas. Komai na su iri ɗaya ne, hatta yanayin abincinsu. Su ma Hausawan na can yanayin mu da su iri ɗaya ne, amma akwai bambanci tsakaninmu da su, musamman ta ɓangaren al’adda. Don haka zan tabbatar ma ta ɓangaren abinci Bahaushe ba shi da matsala. Ni dama ba ni da abincin da ya wuce tuwo, kuma a can ma ina samun irin wanda na ke so.

Wata kila ba za ki rasa wani mafarki da ki ke da shi, wanda kike fatan ya zama gaske?
Ina son in kafa gidauniya, domin yanzu haka ma ina da gidauniya da na ke koyawa mata sana’ar hannu, ina koyar da man shafa da gwadawa mata kwalliya, domin su zama ma su dogaro da kansu. Wannan wani dogon burina ne na fara kafawa, idan Allah ya sa mun kafa gwamnati a shekarar 2023, Ina fatan gwamnatin mu ta yi amfani da waɗannan mata, ta kafa su, ta hanyar ba su jarin da za su dogara da kan su har ma wasu su dogara da su. Kuma ta yi amfani da su wurin kafa ƙananan masana’antu don amfanar mata na karkara da ma na cikin birnin da ke da ƙarancin hali da kuma tallafa wa marayu.
 
Ta ɓangaren siyasa, wace shawara za ki ba wa ‘yan siyasa kan ba wa mata dama a siyasa?
‘Yan siyasa su yi amfani da ƙungiyoyin mata ‘yan siyasa wajan ƙara wa matan ƙarfin gwiwa. Su taimaka wa mata don samun cikar burinsu ta fuskar siyasa. Kuma idan mulki ya sake dawowa gun mu, za mu roƙi gwamna ya sa majalissar dokoki ta Jihar Jigawa ta qara wa dokar ma su yin fyaɗe ƙarfi, a riƙa yiwa waɗanda suka aikata laifin horo mai tsanani.

Mene ne shirinku ga al’umma idan kun samu kujerar mulki?
Idan Allah Ya nufe mu da samun gwamnati, za mu sa ido ne mu ga gwamnati ta fara tallafa wa mata da marayu. Kuma za mu yi bincike mu ga abinda mata suka fi buƙata a lokacin sai mu sa gwamnati ta taimaka ma su idan lokacin ya yi.

Me ki ka fi so a rayuwa?
Na fi son zanan lafiya, ba na son fitina, ba na son tashin hankali. Kuma ina son na ga ina taimaka wa al’umma sosai.

Me ya fi ɓata miki rai?
Ba na son ƙazafi, ƙarya ko munafurci.

Mata ‘yan kwalliya ne. Wacce kwalliya ce ba kya gajiya da ita?
Ya danganta da yanayi, kwalliyar zuwa gidan jana’iza ta sha bamban da ta gidan biki, haka ta salla ita ma daban ta ke. Duk yanayin da na samu kaina akwai irin kwalliyar da na ke yi, kuma duk wadda na yi tana yi min daidai. Ya danganta da yanayin da na samu kaina a ciki.

Daga ƙarshe mene ne saƙonki ga mata ‘yan’uwanki?
Saƙona shi ne; ‘Yan’uwana mata su tashi tsaye su yi sana’a, domin sana’a dole ce wajan ‘ya mace, saboda matar da ba ta yin sana’a ta zama jaka. Ita mace mai yin sana’a ko wajan miji tafi daraja, domin tana da bambanci da matar da ba ta yin komai, saboda ita ko wajan lura da gida tana iya taimaka wa miji a samu rufin asiri wajan cigaban gidan. Matar da ta ke tallafa wa miji kuwa ko ta vangaren sirikanta wato iyayan miji matsayin ta na daban ne. Darajarta nesa ta fi ta wadda sai ya ba ta ta ke komai. Ita rayuwa da mu ke gani, musamman ta aure tana buqatar taimakekeniya, taimakeni, intaimakeka. Miji ne Allah ya ɗora wa kula da mata, amma idan mata ta taimaka zai ƙara wa zamansu inganci.
 
Hajiya, na gode.
Malam, ni ma na gode sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *