Numfashin mutum (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, assalam aliakum. Barkan mu da wannan lokaci kuma barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka na Jikin ɗan Adam, wanda ya ke kawo mu ku bayanai game da jikin bil adama, domin ku fa’idantu, ku san yadda jikinku ya ke aiki.

Har yanzu dai muna magana ne akan yadda ɗan Adam ke numfasawa, da kuma abubuwan da ke faruwa yayin wannan numfashi. Ɗan Adam na fara numfashi ne yayin da aka Haife shi, baya daina har sai kwanansa ya ƙare. Yayin da ɗan Adam ke cikin mahaifiyarsa, ba ya numfashi duk da cewa yana da huhu. 

Yadda abin yake shi ne, lokacin da ɗan tayi yake ciki, huhu na fara bayyana ne lokacin da yake ɗan sati shida. Ɗan tayin yana ƙara girma, shima huhun ya na ƙara girma da haɓaka. Yayin da tayin ya kai wata shida zuwa takwas, huhun ya kai matuƙa a girma, kuma idan ya kasance an haifi yaron a wannan lokaci, zai iya rayuwa amma cikin kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya. 

Yaro ɗan wata tara Wanda yake ciki kafin a Haife shi, huhunsa ya girma kuma za a iya numfashi da shi amma cike yake da ruwa wanda ake Kira da “aminotic fluid “, to saboda haka ba zai iya numfashinba. Amma da zarar ya rage saura ‘yan daƙiƙu a haifi yaron, wannan ruwa yana bin hanyoyin jini. A yayin da ake haifar yaron ko yarinyar, matsuwa da yaron ke shiga yayin da ya biyo kafar haihuwa ke sa a matse ƙirjinsa ta yanda hakan zai takura huhun yaron. Hakan sai ya sa ruwan da ke cikin huhun ya biyo hanyar baki da hanci. Wannan wata hanyar ce da shi ruwan ke fita daga cikin huhu. 

Yaro na fara numfashi ne lokacin da aka Haife shi. A lokacin da yake ciki, musayar iska na faruwa ne tsakanin yaron da mahaifiyarsa ta hanyar igiyar cibiya. Idan anyi haihuwa, ana yanke cibiya kamar yadda duk muka sani. Yanke cibi zai katse musayar iska tsakanin uwa da ɗanta, to hakan zai sa yaron ya fara dogaro da iskar duniya, to tun daga nan numfashi ke farawa. 

Amma kafin hakan, bari na ƙara muku bayani: da zarar an yanke cibiya, iskar oksijin za ta daina isa izuwa gaɓɓai, ciki har da ƙwaƙwalwa. To da yake cibiyar kula da numfashi a ƙwaƙwalwa take,  kuma abinda ke ingiza wannan cibiya ta ƙara aiki wajen numfashi abu uku ne: ƙarancin iskar oksijin, hauhawar iskar kabon dai ogzayid, da kuma yawan sinadarin acid a cikin jini.

To da zarar an yanke cibiya,  iskar oksijin da uwa ke shaƙa, wadda ke shiga ta igiyar cibiya ta kai ga yaron za ta daina zuwa, shi kuma yaron iskar kabon dai ogzayid da ya kamata ta baro jikinsa ta biyo igiyar cibiya ta shiga jikin uwa domin a fitar da ita za ta rasa hanya saboda an yanke cibiya. Da zarar hakan ta faru, sai ƙwaƙwalwa ta kunna cibiyar kula da numfashi ta yaron. Za a aiko saƙo daga wannan cibiyar numfashi izuwa huhu ana umartarsu da su buɗe kafafen da iska za ta shigo. 

Hakan ba faruwa ne cikin ƙanƙanin lokaci bayan an yanke wa Jariri ko jaririya cibiya. Shikenan sai yaro ya kama numfashi Wanda Wanda zai yanke ba sai dai in wata matsala ta faru, ko kuma mutuwa.  Wannan shi ne bayani game da asalin yadda numfashi ya samu tun muna jarirai! Wani aikin sai Sarkin halitta! 

Mun sano cewa Numfashi na ɗaya daga cikin abubuwan da ɗan adam yake yi kullum, ba tare da ya damu da yasan me ke faruwa a lokacin da yake numfashin ba; wato hankalin sa ko hankalin ta ba ya kan numfashin , har sai sun samu kan su a wani hali da kan iya sanya yanayin numfashin ya canza. Misali: mura mai sanya toshewar hanci. Kaga mutum zai iya ƙorafin cewa: “ba na iya numfashi”. Amma duk da haka kuma, ba lallai yaa san abin da ke wakana ba yayin faruwar hakan. 

Ɗan adam yana numfashi sau 18 zuwa sau 20 a cikin minti guda, wato kimanin sau 1000 zuwa 1200 a duk awa guda, sannan sama da sau dubu ashirin da biyar a kowacce rana. Sau nawa ki ka/ ka taɓa godewa Sarkin halitta akan wannan? Masana jikin mutum sun ƙiyasta cewa mutum yana numfashi cikakke guda daya a duk bayan bugun zuciya guda hudu.

Na zauna na yi amfani da agogo, na kimanta sau nawa nake numfashi a duk minti guda, a inda na gano cewa: ina numfasawa sau 19 a duk minti daya. Ina ganin zai yi kyau kaima/ke ma ku zauna ku ƙirga naku, saboda za mu ƙara tabbatar da cewa jikinmu na aiki tuƙuru, sannan kuma za mu godewa Wanda ya ƙera mana jikin.

Babban maƙasudin da yasa jiki ke buƙatar numfashi shi ne: Shigar da iskar oksijin cikin jiki, saboda kwayoyin halitta su hada ta da amfanin da suka zuko daga cikin abinci domin su samu kuzarin gabatar da ayyuka  DA kuma fitar da iskar kabon dai ogzayid daga cikin kwayoyin halitta izuwa iskar da ke duniya, domin wannan iska ta kabon, ta kasance guba ga kwayoyin halittu, duk da cewa su ne ke samar da ita. Wannan ya yi daidai da ace barin bayan gari a jiki ba tare an fitar da shi ba, kan iya jawo illa ga jikin ɗan adam.

Numfashi yana da manya-manyan amfani guda biyar:
1.Tabbatar da shige-da-ficen iska ciki da wajen huhu. 2. Kiyaye hanyoyin da iska ke bi daga illolin sauyawar zafin yanayi, da makamantan su.

  1. Bada kariya ga hanyoyin iska ga barin illatuwa daga ƙwayoyin cuta da kan iya kurɗawa hanyoyin iska.
  2. Samar da sautin da zai tashi magana, waƙa, da sauran hanyoyin da muke bi domin isar da saqo ta hanyar sauti, misali; gyaran murya.
    5.Fayyace wari ko kamshi. Wannan yana karkashin kulawar kwayoyin halitta na musamman da ke cikin kogon hanci.

Kamar yadda na yi bayani a wancan satin, iskar da ke duniya cike take da sinadarai kala-kala. Amma jikin ka ya ƙware matuka wajen zaƙulo iskar oksijin kaɗai, ya bar ragowar. Tambayar a nan ita ce: waɗanne hanyoyi ne jiki ke bi domin ya shigar da iskar oksijin cikin jiki, sannan ya fitar da iska mara kyau, wato iskar kabon dai ogzayid daga cikin jiki? Biyo ni sannu a hankali domin samun amsar wannan tambaya.

Mu haɗu sati mai zuwa idan Sarkin ya kaimu, domin kawo muku bayanin yadda numfashi ke kasancewa, da rawar da wadannan iskoki kala biyu ke takawa domin kasancewar mu a raye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *