Macron na son a bai wa Afrika babban matsayi a G20

Daga AISHA ASAS

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana goyon bayansa kan bai wa Tarayyar Afrika kujerar din-din-din a ƙungiyar G20 ta mafiya warfin tattalin arzikin duniya, kwatankwacin wadda Tarayyar Turai ke da ita.

A jawabinsa gaban manema labarai a tsibirin Bali, shugaba Macron ya ce, kamar yadda Ƙungiyar Tarayyar Turai EU ke da ta cewa, a cikin G20 kamata ya yi ita ma AU ta samu makamancin matsayin.

Zuwa yanzu dai Afrika ta Kudu ce ƙasa ɗaya tilo daga nyahiyar Afrika da ke cikin ƙungiyar ta G20, guda cikin manyan ƙungiyoyi da ke cimma matsaya game da muhimman batutuwan duniya.

Shugaba Macky Sall na Senegal da ke jagorancin Ƙungiyar Tarayyar Afrika, ya buƙaci samun wakilcin ƙassahen Afrika a manyan hukumomin da suka ƙunshi kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma G20.

Sall da shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta Kudu da ke halartar taron na G20 a tsibirin Bali na Indonesiya ko cikin watan Oktoba sun nanata buƙatar cewa, wajibi ne manyan ƙasashen duniya su girmama muradan kowanne sashe ko kuma fuskanci haɗarin yankan kauna.

Macron a jawabin da ya gabatar, ya bayyana shirin kiran wani taron ƙasa da ƙasa kan sabuwar hulɗar kasuwancin Faransa da Afrika ta Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *