Gwamna Buni ya tallafa wa marayu 200 da Naira 50,000 kowanne

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya umurci Ma’aikatar Ƙirƙiro Hanyoyin Tattalin Arziki da Ayyuka ta bai wa zawarawa 400 tallafin dogaro da kai.

Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Asabar a lokacin da ya karɓi baƙuncin marayu 200 daga ƙananan hukumomi 17 dake faɗin jihar.

Bugu da ƙari kuma, gwamnan ya tallafa wa kowane maraya ɗaya daga cikin adadin marayu 200 da kyautar Naira 50,000, sannan kuma shaidar da cewa sun cancanci kulawar gwamnati da sauran al’umma baki ɗaya.

Ya ce ya zama dole a tallafa musu tare da bai wa marayu da sauran marasa galihu a nuna musu ƙauna ta musamman.

“Haka zalika, mun yanke shawarar tallafa wa marayun, zawarawa a cikin sauran ƙungiyoyi maras galihu, ta hanyar ba su jari don samun dogaro da kai.

“Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe don taimakawa waɗanda suka rasa iyayensu, musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su na tsawon shekaru goma da aka kwashe ana fama da tashe-tashen hankula.”

Haka kuma, Gwamna Buni ya yaba wa Gidauniyar Ƙatar bisa tallafin kayayyakin more rayuwa ta take raba wa ga marayu da marasa galihu a faɗin jihar.