Ya zama dole Gwamnatin Tarayya ta bunqasa kiwo a Nijeriya – Sanata Lawan

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sha alwashin cewa zauren majalisar dattawan Nijeriya zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa harkokin kiwon dabbobi a ƙasar nan a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan ci gaban tattalin arzikin ƙasar nan.

Sanata Lawan ya sanar da hakan a ƙarshen mako, a sa’ilin da yake ƙaddamar da allurar rigakafi ga dabbobi kyauta a qauyen Jajuwa da ke ƙaramar hukumar Jakusko a jihar Yobe; shirin da Gidauniyar SAIL Foundation a ƙarƙashin sa ke ɗaukar nauyin gudanar da shi tun shekarar 2018, domin al’ummar mazabarsa.

Ya ce harkokin kiwo a Nijeriya ba ƙashin yasarwa ba ne, a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan kadarkon da ke ɗauke da tattalin arzikin Nijeriya, “wanda kuma ya dace gwamnati ta tallafa wa harkar kiwo, saboda muke cin gajiyar fanni wajen ci gaban tattalin arzikinmu, sannan barinsa haka ba tare da agaza wa ɓangaren ba, to ba a yi masa adalci ba; duk sana’a ce mai zaman kanta, dole a tallafa wa sashen.

“A hannu guda kuma, suma bankuna harkar sana’a ce mai zaman kanta, wanda idan har gwamnati za ta tallafa wa masu tafiar da su ba, ban ga dalilin da za a ki tallafa wa makiyaya dabbobi ba, wanda a zahiri ma su ne suka fi kowa cancanta a tallafa musu, musamman gwamnatin tarayya.”

Sanata Lawan ya ƙara da cewa, “za mu ci gaba da matsa wa Gwamnatin Tarayya lamba har sai ta tallafa wa Fulani makiyaya dabbobi domin rage matsalolin da su ke fama da su lokaci zuwa lokaci.

“Sannan a ƙoƙarinmu, a yau mun zo nan ne domin ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi, waɗanda suka ƙunshi shanu, tumaki, da awakinmu, tare da sauran ƙananan dabbobi a wannan shiyya ta Yobe ta Arewa.

“Wannan biki ne wanda muke gudanar da shi kowace shekara domin yi wa dabbobi allurar rigakafin cutuka daban-daban, wanda a bara mun yi wa dabbobi kimanin miliyan ɗaya da rabi, kuma a wannan shekara ma haka za mu yi. Sannan za mu qara da bai wa Fulaninmu tallafin dusa da sauran abincin dabbobi kyauta, domin rage musu wahalhalu.”