Kenya: CMG ya shirya taro mai taken “Sin da sassan duniya sun kama sabon tafarki”

Daga CMG HAUSA

An gudanar da wani taron karawa juna sani tsakanin kafafen watsa labarai na ƙasar Sin da ƙasashen Afrika, mai taken “Sin da sassan duniya sun kama sabon tafarki”, wanda reshen babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG a Afrika ya karɓi baƙuncinsa a birnin Nairobin ƙasar Kenya jiya.

Shugabannin kafafen watsa labarai da masana da malamai 60, daga ƙasashe 20, da suka hada da Kenya da Rwanda da Tanzania da Madagascar da Sudan ta Kudu da Zambiya da Saliyo ne suka yi tattaunawa mai zurfi, kan maudu’ai da suka haɗa da “ Me sabon tafarkin Sin ke nufi ga nahiyar Afrika” da “Ina batun sabon tafarkin gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai ɗaya” da kuma “Me hadin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai na Sin da Afrika zai samar ga al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai ɗaya”.

Mahalarta taron, sun amince cewa, sabbin ci gaban da ƙasar Sin ke samu bayan babban taron wakilan JKS karo na 20 zai kawo sabbin damarmaki ga Afrika, haka kuma sabon kuzari ne dake ingiza ginin al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai ɗaya.

Baya ga haka, haɗin gwiwa tsakanin kafafen watsa labarai na Sin da Afrika a sabon zamani, na ƙunshe da dimbin damarmaki.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha